Tirela Ta Yi Gaba da Gaba da Karamar Mota, Ta Markaɗe Mutane Har Lahira
- An samu mummunan haɗarin mota tsakanin tirela da mota kirar Honda Accord a hanyar Abuja zuwa Lafiya a yammacin jiya Talata
- Rahotanni sun nuna cewa tirelar ta yi kaca-kaca da mutanen da ke cikin karamar motar ta yadda aka gagara gane fuskokinsu
- Shaidun gani da ido sun bayyana yadda mummunan hadarin ya faru a lokacin da matukin babbar motar ya gagara taka mata birki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Keffi, Nasarawa - An samu mummunan hadari tsakanin wata mota kirar Honda Accord da babbar mota kirar tirela.
Rahotanni sun nuna cewa motocin sun yi karo da juna ne wanda hakan ya jawo mutuwar mutane da jikkata da dama.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne a lokacin da babbar motar ta nufi hanyar Keffi daga Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin haɗarin motar hanyar Keffi
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa hadarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birkin babbar motar.
Waɗanda suke wurin sun tabbatar da cewa matukin babbar motar ya gagara rike ta yayin da yake gangarowa daga tudun Kugbo da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi.
Mutanen da suka mutu a haɗarin
Rahotanni sun nuna cewa tirelar ta markaɗa mutane hudu da ke cikin karamar motar har lahira ta yadda aka gagara gane su.
An kuma ruwaito cewa sauran mutanen da haɗarin ya ritsa da su sun samu munanan raunuka a wurare da dama, rahoton Daily Post.
Jami'an FRSC sun kawo agaji
Biyo bayan haɗarin, jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) sun isa wajen cikin gaggawa domin mika agaji.
Jami'an sun yi kokarin ciro bangarorin mutanen da matar ta markaɗa domin a samu damar musu janaza.
An yi haduran mota lokacin sallah
A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai kula da haɗura ta ƙasa (FRSC) ta fitar da rahoto kan yadda bikin sallah ya gudana a wasu jihohin kudancin Najeriya.
Rahoton da hukumar FRSC ta fitar ya nuna cewa an samu haduran mota da dama wanda ya jawo asarar rayuka da jikkata mutane da yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng