'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 6 Yayin Wani Hari a Kaduna
- Ƴan bindiga ɗauke da manyan muggan makamai sun kai sabon hari a jihar Kaduna inda suka hallaka bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum shida yayin da suka kai hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar
- Shugaban ƙaramar hukumar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ƴan bindigan sun kuma ƙona gidaje a yayin farmakin da suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - An tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bauda da Chibiya a gundumar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Kaduna: Yadda ƴan bindiga suka kai hari
Ƴan bindigan sun kai farmaki a ƙauyukan ne a ranar Litinin da yamma, inda suka kashe mutane tare da ƙona wasu gidaje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Punch ta ce shugaban ƙaramar hukumar, Ibrahim Gajere, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne kan babura ɗauke da manyan muggan makamai inda suka kashe mutum biyu a Bauda da wasu mutum uku a Chibiya.
A cewar shugaban ƙaramar hukumar, an kuma ƙona gidaje bakwai tare da babura takwas.
"Ko da yake akasarin waɗanda aka kashe, an kai musu hari ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu, an kashe mutum biyu a gidajensu."
"An sanar da jami’an tsaro faruwar lamarin kuma sun tsananta yin sintiri a cikin yankin da kewaye."
- Ibrahim Gajere
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Ƴan bindiga sun sace ƴan ƙasar waje
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da shugaban kamfanin Fouani mai wakiltar LG da Hisense a Legas.
Ƴan bindigan sun sace manajan ne tare da wasu ƴan kasar Lebanon guda uku a yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale a Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng