"Ba a Nan Kawai Ake Wahala ba," Shugaba Tinubu ya Gargadi Jama'an Najeriya

"Ba a Nan Kawai Ake Wahala ba," Shugaba Tinubu ya Gargadi Jama'an Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta ba su kadai ba ne, domin sauran kasashen duniya na fuskantar irin wannan kalubale
  • Shugaban ya shaida haka ne ga tawagar ‘yan majalisa karkashin jagorancin shugaban majalisa, Godwill Akpabio yayin ziyarar barka da sallah da su ka kai masa a Legas
  • Bola Tinubu na ganin za a iya shawo kan matsalolin da ake fuskanta matukar al’umar gari sun bayar da hadin kai, inda ya yi gargadi ga masu lalata kayan amfanin gwamnati su daina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lallabi ‘yan Najeriya da cewa ba a kasar nan kadai ake shan wahala da matsin da ake kokawa a kai ba, sauran kasashen duniya na fuskantar yanayin.

Kara karanta wannan

Ana cikin talauci, Tinubu ya fadi hanyar da za ta zamo mafita ga 'yan Najeriya

Amma ya na ganin duk da cewa gwamnatinsa ta gaji tarin matsalolin tattalin arziki masu wahalar magani, za a kawo gyara kuma ba zai taba watsi da al’amarin jama’ar kasar nan ba.

Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya ce ana shan wahala a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Vanguard News ta tattaro cewa shugaban ya bayyana haka ga wasu ‘yan majalisa karkashin jagorancin Godswill Akpabio da Barau Jibrin da su ka kai masa ziyarar barka da sallah a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan Najeriya su tallafa a kawo sauyi,” Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da cewa ‘yan Najeriya sun shiga kangin wahala, amma lamarin na bukatar taimakonsu domin a warware matsalolin da ake fuskanta.

Punch News ta wallafa cewa Shugaban ya bayyana dole a lalubo hanyoyin kawo karshen ta’addanci domin samar da dama ga manoma su wadata kasa da abinci.

Ya gargadi ‘yan Najeriya masu lalata kayan amfanin al’umma kamar cire wayoyin wutar lantarki da lalata hanyoyin jiragen kasa su daina abin da zai kawo nakasu ga tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

“Za a samu sauki zuwa Disamba”, Tinubu

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da yunwa za su yi sauki a cikin shekarar 2024 da ake ciki.

Shugaban ya nemi hadin kai da taimakawa manufofin gwamnati domin cimma fatan da ya ke da shi, inda ya kara da cewa tattalin arziki zai daukaka matukar aka samu hadin kan da ake bukata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.