EFCC Na Tsaka da Neman Yahaya Bello, Gwamnan Kogi Ya Aikawa Uban Gidansa Wasiƙa

EFCC Na Tsaka da Neman Yahaya Bello, Gwamnan Kogi Ya Aikawa Uban Gidansa Wasiƙa

  • Gwamna Usman Ododo, ya jinjinawa magabacinsa, Yahaya Bello, bisa kyakkyawan jagoranci da kuma kawo sauyi a jihar Kogi
  • Ododo ya kuma bayyana Bello a matsayin babban jigo a siyasar jihar yayin da yake taya shi murnar cika shekaru 49 da haihuwa
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumar EFCC ke ci gaba da neman tsohon gwamnan na Kogi domin mika shi gaban kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, ya jinjinawa magabacinsa, Yahaya Bello, bisa kyakkyawan jagoranci wanda ya haifar da sauyi a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba wa Ododo shawara kan harkokin yada labarai Ismaila Isah ya fitar jiya a Lokoja a bikin cikar Yahaya Bello shekaru 46 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kwankwaso ya tona asirin masu zuga Aminu Ado, ya fadi shirinsu

Gwamnan Kogi ya yi magana kan Yahaya Bello
Kogi: Usman Ododo ya taya Yahaya Bello murnar cika shekaru 49 da haihuwa. Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Ododo ya taya Bello murnar cika 46

Ododo ya kuma bayyana Yahaya Bello a matsayin babban jigo a siyasar jihar yayin da yake taya shi murnar cika shekaru 49 da haihuwa, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Yahaya Bello babban jigo ne kuma ya tallafawa masu karamin karfi zuwa matsayi mai girma yayin da ya daga darajar jihar a shekaru takwas da yayi kan mulki.

Ododo ya yi ruwan yabo ga Yahaya Bello

A wasikar taya uban gidansa murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Ododo ya ce:

“Ina cike da godiya bisa jajircewa da sadaukarwar da ka nuna domin mu kasance a inda muke a yau da kuma turba mai kyau da ka dora jiharmu da al’ummarmu a kai.
"Ina yi maka fatan karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya da wadata, kuma ka kasance cikin farin ciki kamar yadda ka saka hakan a fuskokin mutane da yawa."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Sarki Sanusi ya tura sakwanni biyu ga Kanawa a ranar sallah

Jaridar PM News ta ruwaito gwamnan wanda ya ce da bazar Yahaya Bello ya ke aka rawa, ya kuma yi addu’ar Allah ya kare rayuwar tsohon gwamnan.

EFCC ta kasa cafke Yahaya Bello

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta iya kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ba.

EFCC ta ce wasu manyan Najeriya ne ke ba Yahaya Bello kariya daga kokarinta na gurfanar da shi gaban kotu kan zargin karkatar da Naira biliyan 80.2 a lokacin da ya ke gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.