Allahu Akbar: Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Allahu Akbar: Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ta Rigamu Gidan Gaskiya

  • Rahotannin da muka samu na nuni da cewa Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki rasuwa
  • An ce Misis Florence Morenike Saraki ta rasu ne a ranar Talata, 18 ga watan Yunin 2024 bayan an garzaya da ita wani asibitin Legas
  • Jim kadan bayan rasuwarta, Dakta Bukola Saraki ya fitar da sanarwa kan abin da ya shafi lokacin da za a yi wa mahaifiyar tasu jana'iza

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Yanzu muke samun labarin rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bulola Saraki, watau Madam Florence Morenike Saraki.

Rahotanni sun bayyana cewa mahaifiyar fitaccen ɗan siyasar ta koma ga mahaliccinta ne tana da shekaru 88 a duniya.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An bayyana jihar da Shugaba Tinubu zai yanka ragon layyarsa

Bukola Saraki ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa
Allah ya yi wa mahaifiyar Bukola Saraki rasuwa. Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

Dakta Abubakar Bukola Saraki ne ya fitar da sanarwar mutuwar mahaifiyarsa, Cif Misis Florence Saraki a shafinsa na X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Bukola Saraki ya ce:

"Cikin bakin ciki da mika lamura ga Allah, ina sanar da rasuwar mahaifiyata, Cif Misis Florence Morenike Saraki, wanda ta rasu a yau Talata, 18 ga watan Yunin 2024."

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce nan gaba kaɗan za su sanar da bayani na lokacin jana'izar mamaciyar tare da godiya ga wadanda suka yi masu ta'aziyya.

Duba sanarwar a nan ƙasa:

Abin sani game da rasuwar Florence Saraki

A hannu daya, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa marigayiyar ta fada doguwar suma ne kafin a garzaya da ita wani asibitin jihar Legas kan ciwon da ya shafi tsufa.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Wasu daga cikin ‘ya’yan masarautar Saraki da suka so a sakaya sunansu sun tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a garin Ilorin a daren jiya.

Marigayi Florence ita ce matar Olusola Saraki, wande ya kasance sanata a Jamhuriyar Najeriya ta biyu kuma jigon siyasa a jihar Kwara har zuwa rasuwarsa a shekarar 2012.

Jarumar fim, Stella Ikwuegbu, ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 16 ga watan Yunin 2024.

Kamar yadda aka ruwaito, an ce Stella ta mutu ne sakamakon ciwon daji da ya cinye kafarta kuma mutuwarta ta jefa mutane cikin jimami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.