Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki

Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki

Da alamu rigimar Bukola Saraki da kuma gwamnatin jihar Kwara ta canza salo bayan da aka fara shirin sauyawa jami’ar gwamnatin jihar suna a makon nan.

Kamar yadda mu ka samu labari ‘yan majalisar dokokin Kwara sun canzawa jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta Kwara suna a Ranar Talatar nan da ta wuce.

‘Yan majalisar dokokin jihar sun yi wa dokar da ta kafa jami’a jihar garambawul domin shafe sunan tsohon gwamnan daga cikin sunan jami’ar gwamnatin jihar.

Wannan ya na cikin dokoki hudu da majalisar Kwara ta yi wa kwaskwarima a zaman da ta yi a farkon makon nan. Yanzu ana jiran gwamna ya sa hannu a kudirin.

Da zarar gwamna ya rattaba hannu, sunan ya shiga doka. A cewar majalisar, kudirorin za su taimakawa ilmi kuma sha’anin shugabancin kananan hukumomi.

Majalisar jihar ta fitar da gajeren jawabi bayan ta yi wannan aiki, ta ce:

KU KARANTA: Alkali ya dakatar da Oshiomhole daga shugabantar APC

Jami’ar Abubakar Olusola Saraki ta koma Jami’ar Kwara - Majalisar dokoki

Majalisar jihar Kwara ta na so a canzawa KWASU suna
Source: Facebook

“Kudirin jami’ar Jihar Kwara na 2020, da ya canza sunan jami’ar daga jami’ar Abubakar Sola Saraki zuwa jami’ar jihar Kwara ya samu karbuwa a gaban majalisa.”

‘Yan majalisar su ka kara da cewa: “An mikawa Mai girma gwamna wannan kudiri domin ya sa hannu.” Da zarar gwamna ya sa hannu, jami’ar za ta canza suna.

Dr. Bukola Saraki ne ya gina wannan jami’a a Garin Malete a 2009 lokacin ya na gwamna. Saraki ya yi mulki a Kwara daga 2003 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar PDP.

Bayan ya sauka daga kujerar gwamna, Saraki ya tafi majalisar dattawa. Saraki wanda ya bar PDP a 2014 ya sake dawowa jam’iyyar a 2018, amma ya fadi zaben 2019.

Ana zargin cewa rigimar tsohon shugaban majalisar da sabon gwamnatin jihar Kwara ta APC ta na cikin abin da ya sa majalisa su ka fara shirin canzawa jami’ar suna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel