Gwamna Fubara Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Shiryawa Kan Magoya Bayansa

Gwamna Fubara Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Shiryawa Kan Magoya Bayansa

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi zargin cewa akwai shirin da ake shiryawa a jihar na ganin an cafke magoya bayansa
  • Gwamna Fubara ya bayyana cewa ko kaɗan ba zai amince da hakan ba saboda magoya bayan na sa suna goyon bayan gaskiya ne
  • Magoya bayan gwamnan dai sun fito ne sun nuna adawa da shugabannin ƙananan hukumomin jihar waɗanda wa'adinsu ya ƙare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers -Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya ce ana shirin damƙe wasu magoya bayansa a jihar.

Magoya bayan gwamnan dai sune suka fito suka nuna adawa da shugabannin ƙananan hukumomin da wa'adinsu ya cika ranar Litinin.

Gwamna Fubara ya yi zargin ana shirin cafke magoya bayansa
Gwamna Fubara ya ce ana shirin cafke magoya bayansa a Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Ana shirin cafke magoya bayan Fubara

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taro da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, gwamnan ya sha alwashin tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo a jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi alƙawarin kare magoya bayansa waɗanda ya ce suna a kan bayan gaskiya.

Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa ba za su amince da shirin da ake yi na cafke magoya bayansa ba, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Me Gwamna Fubara ya ce kan ciyamomi?

Gwamna Fubara ya bayyana cewa babu ƙarin wa'adi ga zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin, inda ya ƙara da cewa doka ta gama bayani a kan hakan.

"Ina sane da cewa akwai shirin da ake yi na zuwa a cafke magoya bayanmu. A wannan karon sai dai a fara da ni kafin a cafke su domin ba na tunanin sun aikata wani laifi. Suna bayan gaskiya ne."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

"Idan har za mu rasa ranmu domin tsayawa bayan gaskiya, za mu yi hakan. Kuma ni ne zan jagoranci yin hakan."
"Bari na ba da tabbaci ga kowa, musamman mutanen Rivers masu son zaman lafiya, doka ita ce doka. Doka ta ce babu ƙarin wa'adi a gare su."

- Siminalayi Fubara

An ba Gwamna Fubara shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya a jihar Rivers ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya binciki shugabannin kananan hukumomi masu barin gado.

Kungiyar Rivers Development Foundation (RiDeF) ta ce akwai zargin karkatar da kudi daga asusun ƙananan hukumomi kan shugabannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel