Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Yi Martani Kan Zargin Kwankwaso Na Sanya Dokar Ta Ɓaci

Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Yi Martani Kan Zargin Kwankwaso Na Sanya Dokar Ta Ɓaci

  • Bayan zargin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kan shirin dokar ta ɓaci a Kano, rundunar ƴan sanda a jihar ta yi martani
  • Rundunar ta musanta zargin inda ta ce ta himmatu wurin kare lafiyar al'umma da kuma dukiyoyinsu ba tare da son kai ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar jihar bayan tube Aminu Ado Bayero kan karaga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta yi martani kan zargin sanya dokar ta baci a jihar.

Rundunar ta musanta zargin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi na cewa ana son kwace mulkin jihar wurin sanya dokar ta ɓaci

Kara karanta wannan

Dubun kasurgumin dan ta'adda ya cika a Yobe, 'yan sanda sun bayyana abin da ya aikata

Yan sanda sun magantu kan zargin Kwankwaso game da dokar ta ɓaci
Rundunar ƴan sanda ta musanta zargin Kwankwaso kan dokar ta ɓaci. Hoto: @masarautarkano, @hrhBayero.
Asali: Twitter

Ƴan sanda sun magantu kan zargin Kwankwaso

Kwamishinan ƴan sanda, Hussaini Gumel shi ya tabbatar da haka a yau Talata 18 ga watan Yuni, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumel ya ce rundunarsu ta kasance a tsakiya ba tare da goyon bayan wani bangare ba a rigimar sauratar jihar.

Ya ce babban burin rundunar shi ne kare lafiya da kuma dukiyoyin al'ummar jihar baki daya, cewar Daily Nigerian.

Kwamishinan ya ce ƴan sanda sun samu akalla umarnin kotuna biyar dangane da dambarwar sarautar jihar da ake yi a halin yanzu.

"Batutuwan suna gaban Babbar Kotun Tarayya da kuma na jihar, muna jiran hukuncin da za su yanke ne."

- Hussaini Gumel

Kwankwaso ya zargi Bola Tinubu rigimar Kano

Wannan na zuwa ne bayan zargin Rabiu Kwankwaso kan kokarin sanya dokar ta ɓaci a jihar da Gwamnatin Tarayya ke yi.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Kwankwaso ya zargi gwamnatin da kin kwashe jami'an tsaro da suka jibge da ke gadin Aminu Ado Bayero duk da tube shi a sarauta a watan Mayun 2024 da muke ciki..

Tinubu ya musanta sanya dokar ta ɓaci

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya musanta zargi shirin sanya dokar ta ɓaci a jihar Kano kan rigimar sarautar jihar.

Tinubu ya ce babu kamshin gaskiya kan zargin Sanata Rabiu Kwankwaso na cewa da hannunta a rigimar da ke faruwa a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel