Wike vs Fubara: Fusattatun Matasa Sun Fatattaki Shugaban Karamar Hukuma Daga Ofis

Wike vs Fubara: Fusattatun Matasa Sun Fatattaki Shugaban Karamar Hukuma Daga Ofis

  • Sabanin siyasa tsakanin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara ya sake ɗaukan sabon salo inda ya shafi shugabannin ƙananan hukumomi
  • Wasu shugabannin kananan hukumomi sun yi alwashin cigaba da aiki duk da cewa kwanakin da doka ta ba su sun kare
  • Matasa sun fatattaki wani shugaban ƙaramar hukuma mai goyon bayan Wike yayin da ya yi yunkurin shiga ofis a yau Talata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Rikicin siyasa da yake faruwa tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya canza salo.

A wani sabon salo da rikicin ya dauka ya shafi shugabannin ƙananan hukumomi da gwamna Siminalayi Fubara ya umurci su sauka daga matsayinsu.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke bayan gwamna ya kori shugabannin kananan hukumomi, sun ja daga

Fubara da Wike
Matasa sun fatattaki shugaban karamar hukuma mai goyon bayan Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wasu fusattatun matasa sun fatattaki shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON) na jihar yayin da ya yi yunkurin shiga ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikincin ƙananan hukumomi a Ribas

A jiya, Litinin, 17 ga watan Yuni shekarun da doka ta ba shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Ribas ya kare.

Sai dai wasu daga cikinsu sun yi alwashin cigaba da zuwa aiki karkashin wata doka da aka kirkira cewa tun da ba a yi zabe ba an ƙara musu wata shida.

Amma duka da haka Gwamna Siminalayi Fubara bai amince da ikirarin nasu ba kuma ya umurce su da su fice daga ofis.

Matasa sun fatattaki Allwell Ihunda

Shugaban kungiyar ALGON ta jihar, Allwell Ihunda yana cikin masu goyon bayan Wike da suka yi alwashin cigaba da zuwa ofis.

Kara karanta wannan

Ana shagalin Sallah, Bola Tinubu ya fara samun goyon bayan sake neman takara a 2027

Saboda haka a yau Talata ya kama hanyar zuwa ofis inda ya yi karo da wasu fusattatun matasa suka far masa, rahoton Vanguard.

Allwell Ihunda ya shiga mota ya ruga yayin da jami'an tsaro suka yi kokarin tare matasan daga kai masa hari.

Fubara ya yi magana kan Wike

A wani rahoton, kun ji cewa yayin murnar cika shekara daya a kan mulki, gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda aka bar masa tarin bashi.

Gwamna Fubara ya kuma bayyana dalilin da yasa tsohon gwamna Nyesom Wike ya fara yakarsa tun wata uku da zamansa gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel