Sallar Layya: Masana sun Bayar da Hanyoyin Cin Nama ba Tare da Matsala ba

Sallar Layya: Masana sun Bayar da Hanyoyin Cin Nama ba Tare da Matsala ba

  • Musulmi a duniya, ciki har da Najeriya na gudanar da bukukuwan sallah babba da ake ta'ammali da nama fiye da yadda aka saba a sauran watannin musulunci
  • Masana sun yi gargadin wannan lokaci ne da za a iya kamuwa da matsalolin lafiya idan ba a bi hanyoyin da su ka dace wajen gyarawa da dafa naman ba, ciki har da gudawa
  • Dietician Auwal Aliyu Ahmad, masanin lafiya ne ta bangaren abinci a Kano, ya shaidawa Legit Hausa cewa nama na daukar awanni da dama kafin ya narke yadda ya kamata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Yayin da musulmi ke cike da farin ciki, ana ta soyawa da yin tsiren naman layya da aka yanka domin ibada.

Kara karanta wannan

Ana gobe sallah, Bola Tinubu ya tura sako na musamman ga 'yan Najeriya

Sai dai masana a bangaren cimaka sun yi gargadin a bi dokokin kare lafiya.

Naman Sallah
Masana sun bayar da shawarwari kan ta'ammali da naman sallah Hoto: Rabiu Biyora/Amb Katsina
Asali: UGC

Masani ya yi gargadi kan cin nama

Dietician Auwal Aliyu Ahmad da ke Kano ya bayyana cewa duk da yanzu lokaci ne da nama ya wadata ba kamar kullum ba, za a iya samun cututtuka da dama idan ba a dauki wasu matakai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin cimakan ya shaidawa Legit Hausa yadda ya kamata a dauki matakan kare kai idan ana son a kammala sallah ciki lafiya ba tare da barkewar cututtuka ba.

Cin nama da yawa na janyo gudawa

Dietician Auwal Aliyu ya shawarci musulmi su guji cin nama da yawa, sannana su rika bayar da tazara a tsakanin lokutan da su ka ci nama saboda ya narke yadda ya kamata.

"Akwai lokacin da ya ke dauka kafin ya narke a cikin ciki, kamar ya na daukan awa takwas zuwa awa 12 ba kamar sauran abinci ba da ya ke daukan kila awa uku zuwa hudu.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano Sanusi II ya yi yayin da aka yanke hukunci a shari'ar Aminu Ado

- Dietician Auwal Aliyu Ahmad

Ya ce idan aka ci nama har ya yi yawa, akwai yiwuwar kamuwa da amai da gudawa da lalacewar ciki, sannan rashin sarrafa shi da kyau ka iya janyo kamuwa da kwayoyin cututtuka.

Meya kamata a yi da naman sallah?

Likita a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Dr. Sani Giade ya shawarci musulmi su tabbata sun wanke dabbobin layyarsu da kyau domin tsira da lafiyarsu bayan sallah.

Vanguard News ta wallafa cewa ya a guji soya naman rumumus saboda hakan ya na cire alfanun da ke jikinsa, musamman ga masu ajiye naman na tsawon lokaci.

An sace ragon layyar liman

A baya mun kawo labarin yadda wasu su ka rufe idanunsu tare da sace ragon limamin kauyen Mista Ali da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato gabanin yanka.

Malam Haruna Yakub ya yi shelar sace masa ragon bayan ya kammala limancin sallar idi tare da bayyana mamakinsa kan yadda lalacewar ta kai har da sace masa ragon layya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel