Musulmi na Murnar Sallah, Mazauna Kano na Bakin Cikin Kwace Gonakinsu
- Manoma da ke da gonaki a karamar hukumar Kiru sun mika koke ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin wasu jami'an gwamnati da kokarin kwace masu gonakinsu
- Mai magana da yawun kungiyar manoman yankin, Muhammad Sani Abdullahi ne ya fadi zargin da su ke yi wa kwamishinan ma'aikatar noma a jihar Dr, Danjuma Mahmud
- Amma ma'aikatar ta yi martani kan zargin, inda ta ce ba gonakin manoma ta ke kokarin kwacewa ba, burtalai ne da doka ta sahale a kwace domin amfani da su yadda ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Yayin da musulmi a fadin duniya ke ta gudanar da bukukuwan sallah babba, manoma a Dansoshiya da ke karamar hukumar Kiru a Kano sun shiga zullumin yadda ake kokarin raba su da gonakinsu.
Manoman karkashin kungiyar masu gonaki a dajin Dansoshiya da kewaye sun zargi kwamishinan noma da albarkatun kasa, Dr. Danjuma Mahmud ne ke kokarin kwace gonakin.
Daily Trust ta tattaro cewa a zantawarsa da manema labarai, jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Muhammad Sani Abdullahi ya bayyana cewa bai kamata a kore su daga gonakinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun hana miyagu zaman dajin Danshoshiya,” Manoma
Manoman karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano sun bayyana cewa masu gonaki a dajin Danshoshiya na tsorata miyagu daga amfani da dajin wajen ayyukan ta’addanci.
Leadership News ta wallafa cewa manoman ta bakin jami’in hulda da kungiyarsu a yankin, Muhammad Sani Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin da ya ke mika kokensu ga gwamnatin Kano kan kokarin ma’aikatar noma na kwace masu gonaki.
A cewarsa, wannan na daga dalilan da ya sa su ke rokon gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsoma baki wajen hana kwace masu gonakin.
Ma’aikatar noma ta yi martani
A martanin ma’aikatar noma kan zargin cewa kwamishinanta, Dr. Danjuma Muhammad na yunkurin raba manoma da gonakinsu, ta ce zargin ba gaskiya ba ne.
A cewar jami’in wayar da kan al’umma na ma’aikatar, Abba Dalha Soron Dinki, filayen da gwamnati ke kokarin kwacewa na kiwo da ake kokarin dawo da su ga kiwo ne ba na manoma ba.
An raba tallafi ga manoman Kano
A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta raba tallafin kayan noma ga manoman da ke jihar Kano a kokarin ganin an wadata kasa da abinci.
Jami’in kula da shirin gwamnatin tarayya na habaka noman daga ma’aikatar albarkatun noma ta kasa, Aliyu Ibrahim Usman ya ce raba tallafin wani mataki ne na habaka noma a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng