Babbar Sallah: Sarki Sanusi Ya Tura Sakwanni Biyu Ga Kanawa a Ranar Sallah

Babbar Sallah: Sarki Sanusi Ya Tura Sakwanni Biyu Ga Kanawa a Ranar Sallah

  • Sarkin Kano na 16 ya ba Musulmi shawarin su taimaki juna a yayin bikin babbar sallah da ake ci gaba da yi a duniya
  • Ya kuma yi kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya da kaunar juna tare da komawa ga Allah don neman zaman lafiya
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da bukukuwan sallah a yanayi mai ban tausayi duba da yanayin tattalin arzikin kasar

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Mohammad Sanusi II, ya yi kira ga Musulmi su rungumi al'adun taimakon mabukata da kuma zaman lafiya a tsakanin juna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Sunusi ya ba da wannan shawara ne yayin hudubarsa bayan ya jagoranci sallar Eid a Masallacin Jumu'a na Sheikh Ahmad Tijjani da ke Kofar Mata a Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi hawa: 'Yan sanda sun yi magana kan yadda aka yi Sallar Idi a Kano

Sarkin ya jaddada muhimmancin bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), wanda ya jaddada taimakon mabukata, musamman a lokacin bikin babbar sallah.

Sanusi II ya tura sako ga musulman Kano
Sarki Sanusi ya mika sako ga Kanawa ranar sallah | Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Ku ninka yawan addu’o’inku, Sanusi ga Kanawa

Haka kuma, ya yi kira ga jama’a su ninka yawan addu’o’insu don samun zaman lafiya a Jihar Kano da kuma kasar nan baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da fama da ake da matsin tattalin arziki a jiha kamar Kano, an lura mutane da dama sun fito domin gudanar da sallar idin bana.

Ana bikin sallah cikin matsin tattalin arziki

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar yanayi mai kunci a fannin tattalin arziki, inda ake ci gaba da bukuwan sallah a cikin matsin tattalin arziki.

Babban abin da ya fi yiwa ‘yan Najeriya ciwo shi ne, yadda kayan abinci ke kara hauhawa da kuma faduwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: NDLEA ta kama miyagun kwayoyin da aka shirya harkallarsu a sallah a Kano

Ana alakanta hakan da sauyin tattalin arziki da kuma tsadar an fetur da aka samu tun bayan da shugaba Tinubu ya janye tallafi a watan Mayun 2023.

Sanusi ya yi biris da umarnin ‘yan sanda

A bangare guda, Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah domin bukukuwan babbar Sallah.

Sarkin na Kano ya jagoranci sallar idi inda ya yi huduba a masallacin Juma’a na kofar Mata.

An gudanar da Sallar Idi a masallacin Juma'a na Kofar Mata sakamakon ruwan sama da ya mamaye harabar filin Idi wanda hakan ya sanya ba za a iya amfani da shi ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel