Bayan Tsige Mamman Ahmadu, Tinubu Ya Ba Tsohon Kwamishinan Legas Wani Babban Muƙami
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Ayodeji Ariyo Gbeleyi a matsayin shugaban hukumar kamfanonin gwamnati (BPE)
- Mista Gbeleyi kwararre ne a harkokin kudi, kasancewarsa babban akawu kuma kwamishinan kudin Legas daga 2013 zuwa 2015
- Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Tinubu ya bukaci Mista Mamman Ahmadu wanda ke jagorancin hukumar BPP ya yi murabus
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ayodeji Gbeleyi a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kamfanonin Gwamnati (BPE).
A yayin sanar da nadin nasa, Shugaba Tinubu ya nemi sabon shugaban hukumar BPE da ya yi amfani dimbin kwarewarsa wajen gudanar da wannan aiki.
Tinubu ya nada Gbeleyi mukami a BPE
Mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Cif Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Shugaban kasar na fatan Gbeleyi zai inganta hukumar a matsayinta Na cibiyar gwamnati da ke taimaka wa wajen gina al'umma da dorewar kamfanoni.
“Wannan zai kasance ta hanyar haɓaka tattalin arziƙin kamfanoni na masu zaman kansu, tabbatar da daidaiton al’umma da kuma amfani da dukiyar jama’a yadda ya kamata."
Wanene Gbeleyi da Tinubu ya nada?
Mista Gbeleyi sananne kuma kwararre ne kan harkokin kudi kuma wanda ya samu lambar yabo a kan aikin akawu.
Shi mamba ne na kungiyar kwararrun akawun Najeriya (ICAN) da kungiyar kwararru kan harajin Najeriya (CITN).
Har ila yau, tsohon dalibi ne a babbar makarantar kasuwancin London, makarantar gwamnati ta Harvard Kennedy, da makarantar kasuwancin Legas.
Ya kasance shugaban hukumar gudanarwa na babban bankin bayar da lamuni na Najeriya (FMBN) kuma kwamishinan kudin jihar Legas daga 2013 zuwa 2015.
Tinubu ya tsige shugaban hukumar BPP
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci shugaban hukumar sa ido a harkokin saye-saye na gwamnati (BPP), Mista Mamman Ahmadu ya yi murabus.
Tinubu ya umarci Mamman da ya mika dukkanin kayayyakin gwamnati da ke a hannunsa da kuma ragamar ofishinsa ga mafi girman matsayi a hukumar.
Asali: Legit.ng