Sallah: Tinubu Ya Bayyana Abin da Najeriya Ke Bukata Ta Samu Ci Gaba
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura saƙo ga ƴan Najeriya yayin da aka gudanar da sallar Idin babbar Sallah na bana
- Shugaban ƙasan ya buƙaci ƴan Najeriya da su kasance masu sadaukarwa domin ƙasar nan ta samu ci gaban da ake so
- Bola Tinubu ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen taimakon juna da ƙaunar juna tare da sanya kishi da son ƙasa a zukatan ƴan Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana abin da Najeriya take buƙata domin ta samu ci gaban da waɗanda suka kafata suka yi fata.
Shugaban ƙasar ya nuna cewa ƙasar nan na buƙatar ƴan ƙasa masu sadaukarwa domin ta cika wannan mafarkin na waɗanda suka assasata.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala Idin babbar Sallah (Eid-el Adha) na shekarar 2024 a Dodan Barrack da ke Legas, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Tinubu ya ba ƴan Najeriya?
Shugaban ƙasan ya jaddada buƙatar jama’a su bi tafarkin sadaukarwa domin ganin al’umma ta samu ci gaba.
"Zama ɗan ƙasa na gari yana zuwa tattare da nauyi mai girma. A matsayin ƴan ƙasa, me kuke yi domin zama waɗanda za su amfani al'umma? Ku je ku yi sadaukarwa."
"Ku so ƙasarku, ku so maƙwabtanku, ku taimaki juna da abin da kuke da shi sannan ku godewa Allah maɗaukakin Sarki. Abin da ake buƙata kenan."
- Bola Tinubu
An ba musulmi shawara
Tun da farko, yayin da yake jawabi ga masallatan, mataimakin gwamnan jihar Legas, Dakta Obafemi Hamzat, ya nuna muhimmancin haƙuri da juriya.
Obafemi Hamzat ya tunatar da al’ummar Musulmi da su fahimci dalilin yin Idi, wanda ya bayyana a matsayin sadaukarwa da juriya.
Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su ci gaba da zaman lafiya a ƙasar nan, su yi abin da ya dace ga kansu da kuma maƙwabta.
Sanusi II ya yi hawan Sallah
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah a birnin Kanon Dabo duk da umarnin ƴan sanda.
Sarkin ya gudanar da hawan ne kamar yadda aka saba a al'ada bayan ya jagoranci sallar Idi a masallacin Ƙofar Mata da ke cikin birnin.
Asali: Legit.ng