Babbar Sallah: An Bayyana Jihar da Shugaba Tinubu Zai Yanka Ragon Layyarsa

Babbar Sallah: An Bayyana Jihar da Shugaba Tinubu Zai Yanka Ragon Layyarsa

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gudanar da Sallar Idin Layya na wannan shekarar a jihar Legas
  • Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya fitar da sanarwa kan hakan, tare da cewa Tinubu ya bar Abuja ranar Juma'a
  • Al'ummar Musulmi a fadin duniya za su gudanar da Sallar Idi a yau Lahadi, 16 ga watan Yuni, bayan hawan Arfa a jiya Asabar, 15 ga wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja, babban birnin kasar, zuwa jihar Legas a ranar Juma'a gabanin bikin babbar Sallah.

A wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Tinubu zai gudanar da Sallar Idi a Legas.

Kara karanta wannan

Rayuwar Tinubu za ta iya shiga hadari, majalisa ta nemi a siya masa sabon jirgi

Bola Tinubu ya shilla Legas domin gudanar da bikin Sallah
Shugaba Bola Tinubu zai gudanar da hutun babbar Sallah a jihar Legas. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu zai gudanar da bikin Sallah a Legas

Kamar yadda fadar shugaban kasa ta wallafa sanarwar a shafinta na X, an ce Tinubu zai kuma aiwatar da hutun Sallah a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri Ngelale ya kara da cewa shugaban kasar zai gudanar da bikin ne ta hanyar addu’o’i da kuma tunanin hanyoyin ciyar da kasar nan gaba.

Wannan kuwa na daga cikin manufofin Bola Tinubu na kawo sauyi a Najeriya ta tsarin da ya dace da kudurinsa na 'Renewed Hope'.

Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Sallah

Idan ba a manta ba, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024.

A cikin wata sanarwa da kwamitin duban waya na kasa ya fitar a ranar Alhamis din da daddare, Sarkin Musulmi ya ce ranar Juma'a 7 ga watan Yuni ta zama 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Wannan ya biyo bayan wani umarni da jagoran Musulmin Najeriya ya bayar a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, na al'ummar ƙasar su duba jinjirin watan Dhul Hijjah bayan faduwar ranar Alhamis.

An ga watan babbar Sallah a Saudiyya

Tun da fari, mun ruwaito cewa kasar Saudiyua ta sanar da ganin watan Dhul Hijjah tare da ayyana ranar Juma'a, 7 ga watan Yuni a matsayin 1 ga watan ƙarshe na 1445H.

A cikin wata sanarwa da Kotun Koli ta kasar Saudiyya ta fitar, ta ce ranar 15 ga watan Yuni ce za ta kama ranar hawan Arafa yayin da Lahadi za ta zama ranar Babbar Sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel