Ana Dab da Sallah, Hukumar DSS Ta Fitar da Muhimman Sako Ga Musulmai

Ana Dab da Sallah, Hukumar DSS Ta Fitar da Muhimman Sako Ga Musulmai

  • A yayin da ake tunkarar bukukuwan babbar Sallah, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta aika da saƙo ga al'ummar musulmi
  • Hukumar ta buƙace su da su yi taka tsantsan wajen gudanar da ibadah da sauran bukukuwa a.lokacin babbar Sallah
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta haɗa kai da sauran jami'an tsaro domin samar da tsaro a lokacin bukukuwan Sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta shawarci al'ummar musulmi da su yi taka-tsan-tsan lokacin bukukuwan Sallah.

Hukumar DSS ta buƙaci al'ummar musulmin da su lura sosai wajen gudanar da ibadah da bukukuwan babbar Sallah da ke tafe.

DSS ta ba musulmai shawara kan bikin Sallah
Hukumar DSS ta bukaci musulmai su yi taka tsantsan lokacin bikin Sallah Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Hukumar ta kuma bukace su da su kiyaye duk muhimman matakan tsaro domin kiyaye lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Za a fassara huɗubar Arafah zuwa Hausa da wasu harsuna 19 na duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Peter Afunanya, ya fitar a shafin X a ranar Asabar.

Sallah: Wane gargaɗi DSS ta yi?

Peter Afunanya, ya shawarci ma'aikata da masu kula da manyan kantuna, wuraren shakatawa da tashoshin jiragen ƙasa da sauransu da su tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro domin kare lafiyar jama’a.

"Ana shawartar al'ummar musulmi yayin da suke gudanar da ibadah da bukukuwa a lokacin Sallah, da su yi taka-tsan-tsan tare da ɗaukar dukkanin matakan tsaron da suka dace."
"Hakazalika, ma'aikata da masu kula da kantuna, wuraren shakatawa, kasuwanni, tashoshin jiragen ƙasa da sauransu, su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da tabbatar da bin doka da oda da sauran matakan tsaro da ake bukata domin kare lafiyar jama'a."

- Peter Afunanya

Peter Afunanya ya ce hukumar ta DSS za ta haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi yayin bukukuwan Sallah.

Kara karanta wannan

Bayan hana hawan Sallah, NSCDC ta dauki kwakkwaran mataki awanni kafin idi a Kano

Jami'an DSS sun kai samame

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun kai samame wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Ilaro a jihar Ogun.

Jami'an DSS sun kama biyu daga cikin waɗanda ake tuhuma yayin da ake tsaka da shari'a, lamarin da ya haifar da ruɗani da hayaniya a harabar kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel