Aminu Vs Sanusi II: Kotu Ta Shirya Raba Gardama, Za Ta Sanar da Sahihin Sarkin Kano
- Yayin da ake ci gaba da rigimar sarauta, kotu ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar masarautar Kano
- Mai Shari'a Liman na babbar kotun tarayya ya sa ranar 20 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan halascin mayar da Sarki Sanusi II
- Wannan na zuwa ne bayan alkalin ya amince cewa kotun tana da hurumin sauraron ƙorafin Mai Martaba Sarki Aminu Bayero
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukunci kan sahihancin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar Kano.
Kotun ta zaɓi ranar 20 ga watan Yuni, 2024 domin yanke hukunci kan halascin sabuwar dokar masarautar Kano da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.
Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, shi ne ya sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar da lauyan Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan Ɗanagundi Chikaosolu Ojukwu ya shigar da sabon ƙorafi gaban kotun, inda ya nemi ta haramta amfani da sabuwar dokar masarautar Kano, The Nation ta ruwaito.
Ma'ana lauyan na neman kotu ta tabbatar da Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin halastaccen Sarkin Kano, kana ta dawo da sauran sarakuna hudu.
Yadda lauyoyi suka gwabza a kotu
Tun farko dai kotun ta shure buƙatar lauyan shugaban majalisar dokokin Kano da majalisar ita kanta, Eyitayo Fatogun, SAN, wanda ya nemi a rufe kundin shari'ar gaba ɗaya.
Fatogun ya ja hankali tare da ƙoƙarin gamsar da mai girma mai shari'a kan bukatar, inda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yi ranar Alhamis.
A ranar Alhamis da ta gabata kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin Ɗanagundi tun da ya shafi take haƙƙin Sarki Aminu.
Har ila yau Fatogun ya sanar da kotun cewa ya shigar da ƙara gaban kotun ɗaukaka ƙara, ya nemi alkali ya dakatar da yanke hukunci sai kotun gaba ta sanar da matsayarta.
Lauyan Antoni Janar da gwamnatin jihar Kano ya goyi bayan waɗannan ƙorafe ƙorafe da bukatun da Fatogun ya gabatar, cewar Leadership.
Mai shari'a Liman ya yanke cewa daga takardar da waɗanda ake ƙara suka gabatar masa, har yanzun ba a sa ranar shari'ar ba kuma babu shaidar sun ɗaukaka ƙarar.
Sarauta: Kotu ta ci tarar Gwamna Abba
A wani rahoton kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta ci tarar gwamnatin jihar N10m kan rigimar sarauta.
Kotun ta dauki wannan matakin ne sakamakon gwamnatin jihar ta ba da umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Asali: Legit.ng