Jagoran Ɗarikar Tijjaniyya Ya Bukaci Sanusi II Ya Sauka Daga Sarautar Kano? Gaskiya Ta Fito

Jagoran Ɗarikar Tijjaniyya Ya Bukaci Sanusi II Ya Sauka Daga Sarautar Kano? Gaskiya Ta Fito

  • Sheikh Muhammad Mahi Niasse ya nesanta kansa da takardar da ke yawo cewa ya buƙaci Muhammadu Sanusi II ya sauka daga sarautar Kano
  • Kwamishinan addinai na jihar Kano, Sani Auwalu Ahmad ya ce takardar ta jabu ce kuma za su ɗauki mataki kan duk mai hannu a lamarin
  • Ya ce sun sanar da jami'an tsaro su kama duk wanda aka gano yana da hannu a shirya takardar jabun domin doka ta yi aiki a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Babban Khalifan Tijjaniyya na duniya, Sheikh Muhammad Mahi Niasse ya nesanta kansa da takardar da ke yawo cewa ya roƙi Muhammadu Sanusi II ya sauka daga sarautar Kano.

Idan ba ku manta ba wata takarda da aka dangana da iyalan Sheikh Ibrahim Nyass ta buƙaci Mai Martaba Sarki Sanusi II ya bi sawun kakansa, kar ya koma sarauta.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, babbar kotu ta yanke hukunci a shari'ar sarautar Kano

Muhammadu Sanusi II
Shugaban Tijjaniyya ya musanta neman Sanusi II ya hakura da sarautar Kano Hoto: @Masarautarkano
Asali: Twitter

Sanusi II: An karyata takardar da ke yawo

Sai dai da take martani, ƙungiyar Tijjaniya ta bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da aka kirkiro takarda aka jinginawa shugabanta na duniya, Tribune ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan shi ne ƙaro na biyu domin irin haka ta taɓa faruwa a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje, amma duk wanda ya yi wannan ƙarya kar ya zargi kowa ya zargi kansa."

Ibrahim Sanyi-Sanyi ya tabbatar da cewa takardar ta ƙarya ce a shafinsa na Facebook bayan labarin ya fara bazuwa a kafafen yaɗa labarai.

Gwamnatin Kano tace takardar jabu ce

Har ila yau, kwamishinan harkokin addinai na Kano kuma mai magana da yawun jagoran Tijjaniya, Sani Auwalu Ahmad Tijjani ya musanta rahoton.

Sani Auwalu ya bayyana takardar da ta nemi Sanusi II ya sauka daga karagar Sarkin Kano a matsayin jabu kuma ba ta da alaƙa da shugaban Tijjaniyya.

Kara karanta wannan

"Ka bi sawun kakanka," Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass sun aike da saƙo ga Sanusi II

Kwamishinan ya ce:

"Mun ba da sa'o'i 48 ga waɗanda suka shirya wannan takarda su miƙa kansu kuma su mana bayanin wanda ya sa su, idan ba haka ba zamu gurfanar da su a gaban ƙuliya."

Ya ce sun kai rahoto ga jami'an tsaro kuma nan ba da jimawa ba duk wanda ke da hannu zai fuskanci fushin doka domin mun bukaci a kama kowaye.

Kotu ta yanke hukunci a shari'ar sarauta

A wani rahoton kuma babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin da ya shafi haƙƙin Sarki Aminu Ado Bayero.

Mai shari'a Liman Muhammed ne ya yanke wannan hukunci a karar da Aminu Babbba Ɗanagundi ya shigar a zaman yau Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262