Ayyukan Gwamnati Sun Tsaya Cak a Wata Jihar Arewa, Gwamna da Mataimaki Sun Tafi Hajji

Ayyukan Gwamnati Sun Tsaya Cak a Wata Jihar Arewa, Gwamna da Mataimaki Sun Tafi Hajji

  • Gwamnan jihar Neja, mataimakinsa, kakakin majalisa, kwamishinoni da wasu 'yan majalisun jihar sun tafi Saudiya aikin Hajji
  • Babu wani tabbaci da aka samu kan ko gwamnan ya mika mulki ga wani a hukumance kafin tafiyarsa, abin da ya jawo Allah wadai
  • Yayin da PDP ke sukar gwamnan kan karya dokar mulki, jama'ar Neja na korafi kan ba a damu da halin da jihar ke ciki a yanzu ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Neja - Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja; mataimakinsa, Yakubu Garba da kuma kakakin majalisar jihar, Barista Abdulmalik Sarkin-Daji duk sun tafi aikin Hajji.

Haka kuma, da dama daga cikin kwamishinoni da wasu ‘yan majalisar jihar su ma sun tafi aikin hajjin, lamarin da wasu mazauna jihar da jam'iyyar PDP suka yi Allah wadai.

Kara karanta wannan

Cikin gaggawa: Majalisa na neman a saya wa Tinubu da Shettima sababbin jiragen sama

Gwamnan Neja ya tafi aikin Hajji tare da mataimakinsa
Gwamnan Neja ya tafi aikin Hajji ba tare da ya mika mulki ga wani a hukumance ba. Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Gwamna da mataimakinsa sun tafi Hajji

Babu wani tabbaci da aka samu a kan ko gwamnan ya mika mulki ga wani a hukumance kafin ya tafi aikin hajjin, in ji rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce jama'ar jihar na ganin gwamnati da 'yan majalisun sun yi watsi da su, duba da irin abubuwan da suka faru da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Tafiyar gwamnan da wasu manyan jagororin jihar ta biyo bayan wani hatsarin da ya afku a ramin hakar ma'adinai da ya binne mutane da dama.

Wa yake tafiyar da ragamar jihar Neja?

Majiyoyi a Minna sun ce sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Abubakar Usman ne ke gudanar da ayyukan gwamnati tun ranar Litinin.

Sai dai babu wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ba kafafen yada labarai da sadarwa a hukumance ba. Duk wani yunkuri na tuntubar ofishin SSG ya ci tura.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gano halin da miliyoyin dalibai ke ciki bayan an saida makarantu

Hajji: PDP ta yi kaca-kaca da Gwamna

Jam'iyyar PDP a Neja ta caccaki gwamnan jihar, Umar Bago kan tafiyar da ya yi zuwa kasar Saudiyya tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

Da yake magana da jaridar The Cable a ranar Alhamis, shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar jihar Neja, Yahaya Ability ya bayyana lamarin a matsayin abin mamaki.

Shugaban ‘yan adawar ya ce tafiyar gwamnan ba tare da mika ragamar jihar ga mataimakinsa, wanda shi ma ya tafi aikin Hajji ya saba wa sashe na 190 (1) na kundin tsarin mulkin 1999.

Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.25bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ya ba da sanarwar amincewar Bankin Duniya na ba Najeriya bashin $2.25bn.

Wale Edun ya bayyana cewa wannan bashin na $2.25bn zai taimakawa kokarin Najeriya na dawo da tattalin arziki da tallafawa talakawan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.