Siyasa: Jam'iyar PDP tayi babban kamu a Jihar Neja

Siyasa: Jam'iyar PDP tayi babban kamu a Jihar Neja

- Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Neja ta samu karin mambobi wadanda suka sauya sheka

- Jam'iyyar ta samu karuwa ne a taron kaddamar da dan takaran sanata mai wakiltar jihar Neja ta Arewa

- Wadanda suka sauya shekar sun kona tsintsiya tare da baiyana cewar APC jam'iyya ce maras alkibila

Babban jam'iyyar adawa a Najeriya PDP tayi babban kamu a jihar Neja inda ta karbi 'ya'yan jam'iyoyi daban daban ciki harda 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki kimanin mutane 817.

Jam'iyyar ta samu wannan gagarumar karuwa ne a wani taron kaddamar da dan takaran sanata mai wakiltar jihar Neja ta Arewa a zaben 2019 Hon. Muhammad Sani Duba wanda ya gudana a garin Kontagora cibiyar Neja ta Arewa, taron da ya samu halartan shugabannin jam'iyyar na jihar da kananan hukumomi 8 da sauran jiga-jigan jam'iyyar dake shiyyar.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, wadanda suka sauya shekar sun kona tsintsiya tare da baiyana cewar APC jam'iyya ce maras alkibila wacce ba abunda ke cikinta sai tarin yaudara da alkawarurrukan karya wanda tunda aka zabeta ba abun azo agani da ta tsinanawa al'ummar Najeriya.

Siyasa: Jam'iyar PDP tayi babban kamu a Jihar Neja
'Ya'yan jam'iyyun siyasa da suka sauya sheka zuwa PDP har da 'yan jam'iyyar APC

A nasa jawabi, Hon. Muhammad Sani Duba ya baiyana cewar, "Da farko ina godiya ga Allah ina kuma godiya ga daukacin 'ya'yan jam'iyyar PDP akan cancantar da suka ga nayi suka kira woni domin na tsaya takara a karkashin wannan jam'iyya namu mai albarka na PDP".

KU KARANTA: 2019: Jam’iyyar PDP ta bullo da shirin doke APC a zabe mai zuwa

Duba ya kara da cewa, "Galibin 'ya'yan jam'iyyar PDP da suka sauya sheka a baya zuwa APC nan bada dadewa ba zasu dawo gida domin sun gane APC jam'iyya ce maras alkibila, PDP ce kadai jam'iyyar da 'yan Najeriya suka yarda da ita kuma take da kyawawan manufofi na ci gaban kasar nan".

"Domin wadanda aka zaba a jam'iyyar APC zaben tumun dare ne al'umma sukayi karkashin guguwar sakk, kuma gashi a yanzu haka 'yan Najeriya sunyi da nasani zaban wasu shugabannin da suka fito a jam'iyyar", inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel