Nau’ukan Ibada 5 Masu Muhimmanci da Ya Kamata Musulmi Ya Yi a Ranar Arafa

Nau’ukan Ibada 5 Masu Muhimmanci da Ya Kamata Musulmi Ya Yi a Ranar Arafa

  • Ranar Arafa ta wannar shekarar za ta kasance gobe Asabar 15 ga watan Yuni kamar yadda hukumomi kasar Saudiyya suka sanar
  • Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce ranar Arafa rana ce mai muhimmanci da ya kamata dukkan Musulmi su shagala da ibada
  • Sheikh Pantami ya ambaci nau'ukan ibada da aka fi so Musulmai su mayar da hankali a kai da kuma dimbin ladan da za su samu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gobe Asabar, 15 ga watan Yuni mahajjata za su yi hawan Arafa a kasa mai tsarki kamar yadda Saudiyya ta sanar.

Akwai nau'ukan ibada na musamman da aka ware ga Musulmai da ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana ranakun hutun Babbar Sallah a Najeriya

Pantami
Sheikh Pantami ya lissafa ibada da ake son yi ranar Arafa. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin haske kan nau'ukan ayyukan cikin wani bidiyo da Affan Buba Abuya ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimmacin ranar Arafa a Musulunci

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa ranar Arafa ta na da muhimmanci sosai a addinin Musulunci.

Malamin ya ce ranar tana cikin kwanaki mafi daraja a duniya, a cikin ranar aka cika addinin Musulunci kuma ana 'yan ta mutane daga wuta zuwa aljanna a ranar Arafa.

Falalar yin Azumi a ranar Arafa

Sheikh Pantami ya ja hankalin al'ummar Musulmi kan yin azumi a wunin ranar Arafa inda yace yana da fa'ida sosai.

Malamin ya kara da cewa Allah SWT ya yi alkawarin kankare zunubin shekaru biyu ga duk wanda ya yi azumi a ranar.

Muhimmancin yin addu'a a ranar Arafa

Har ila yau Isa Ali Pantami ya kwadaitar da Musulmi kan dagewa da yin addu'a a wunin ranar Arafa.

Kara karanta wannan

Jigon APC, Salihu Lukman ya nakasa jamiyyar bayan ya yi murabus, ya jero dalillai

Shehin malamin ya ce Musulunci ya koyar da cewa mafi alherin addu'a da mutum zai yi ita ce addu'ar ranar Arafah.

Sauran ibadan da ake so ranar Arafa

A karshe Sheikh Pantami ya ce sauran ibada da mutum zai iya yi a ranar akwai karatun Alkur'ani wanda shi ne babban zikiri.

Baya ga haka an kwaidatar a kan gaida maras lafiya, tasbihi, wasu nau'o'i na ambaton Allah SWT da dai sauransu.

An ba mahajjata shawara a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta ambaci adadin mahajjatan da za su gabatar da aikin Hajjin shekarar 2024 yayin da shirye-shirye suka kammala.

Jami'in yada labaran ma'aikatar lafiya ta kasar, Dr. Muhammad Al-Abdullaali ya ambaci babbar matsalar da mahajjata za su iya fuskanta yayin Hajjin bana

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel