Kwanaki da Yin Gyara, TCN Ya Ce Bata Gari Sun Kuma Jawo Katsewar Lantarki a Borno

Kwanaki da Yin Gyara, TCN Ya Ce Bata Gari Sun Kuma Jawo Katsewar Lantarki a Borno

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da an kai hari kan turakan wuta da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe
  • TCN ya ce harin ya sanya jihar Borno komawa cikin duhu kwanaki kadan bayan gyara wutar lantarki a fadin jihar
  • A yayin da jami'an kamfanin ke ƙoƙarin gyara turakan da aka lalata, TCN ya bayyana matakin da zai dauka a kan lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Kwanaki kadan bayan gyara wutar lantarki a Arewa maso gabas an koma gidan jiya a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa an koma cikin duhu a jihar Borno bayan bata gari sun sake lalata turakan wuta da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sarkin Kano na 15 ya rubuta takarda ga ƴan sanda kan hawan sallah

Borno map
TCN ya ce an sake lalata turakan wuta a Borno. Hoto: Legit
Asali: Original

Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ne ya sanar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka lalata wutar lantarkin Borno?

Kamfanin TCN ya sanar da cewa a ranar Talata da misalin karfe 10:15 na dare bata gari suka kai hari kan turakan wuta a yankin Borno.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya yi sanadiyyar lalacewar turakan wuta masu lamba T193 da T194 a tsakanin jihohin Borno da Yobe.

Yadda TCN ya gano an kai harin

Kamfanin TCN ya bayyana cewa ya gano an lalata turakan wutar ne bayan an samu rashin wuta a Maiduguri duk da cewa an harba wutar daga jihar Yobe.

Ana cikin haka sai jami'an kamfanin da jami'an tsaro suka shiga daji suna duba abin da ke faruwa har suka ga an lalata turakan wutar.

Kara karanta wannan

Kotu ta dawo da basaraken da El-Rufai ya tuge, ta ci tarar gwamnatin Kaduna N10m

Ya ake ciki maganar wuta a Borno?

Kamfanin TCN ya ce lamarin ya jawo rasa lantarki a jihar Borno amma za su duba yiwuwar samar da wuta ko ta wucin gadi ce.

TCN ya kuma bayyana cewa ana cigaba da kokarin gyara turakan wutar tare da cewa zai cigaba da ɗaukan mataki domin kare turakan wuta a Najeriya.

Gwamnan Borno ya mika mulki ga mataimakinsa

A wani rahoton, kun ji cewa daga ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, jihar Borno ta samu sabon wanda zai jagoranci gudanar da mulkinta na tsawon kwanaki 28.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya miƙa ragamar mulkin jihar Borno ga mataimakinsa watau Umar Usman Kadafur a yayin da ya tafi aikin Hajji a kasa mai tsarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng