Gwamna Ya Fadi Babban Abin da Ke Kawo Cikas Wajen Murkushe 'Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya koka kan matsalar rashin da ta daɗe tana addabar mutanen jihar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba
- Dauda Lawal ya bayyana cewa ba shi da iko kan harkokin tsaron jihar saboda hukumomin tsaro ba su karɓar umarni daga wajensa
- Ya nuna cewa an kasa shawo kan matsalar ƴan bindiga ne a jihar saboda katsalandan na siyasa da ake sanyawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya ce ba shi da iko kan harkokin tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa iko kan hukumomin tsaro da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda ba a hannunsa yake ba.
Me Gwamna Dauda ya ce ka rashin tsaro?
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana haka ne a wani taro da tashar Channels tv ta shirya domin bikin ranar Dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi Allah wadai da ayyukan ƴan bindiga a jihar, yana mai ɗora alhakin lamarin a kan abin da ya bayyana a matsayin sanya siyasa a ciki.
A cewar Gwamna Dauda Lawal, ana wasa da rayukan mutane masu daraja.
"A suna, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wata hukumar tsaro ta soja, ƴan sanda ko na sibil difens."
"Suna karɓar umarni ne daga wajen manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, na so a ce muna da shi, da ba wannan zancen ake yi ba."
- Dauda Lawal
Me ya hana magance ƴan bindiga a Zamfara?
Ya ce ba a samu wani ci gaba ba kan matsalar tsaro a jihar ba saboda abin da ya bayyana a matsayin katsalandan na siyasa.
A cewar gwamnan, hukumomin tsaro na da dukkan abin da ya kamata domin murƙushe masu aikata laifuka a faɗin ƙasar nan.
"Akwai siyasa a cikin lamarin tsaro a ƙasar nan. Idan da ba mu da wannan matsalar, sojoji za su iya murƙushe kowa."
- Dauda Lawal
Abin da ake gayawa Tinubu kan tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa ba a gayawa Shugaba Bola Tinubu cikakkun bayanai kan matsalar rashin tsaro.
Gwamna Dauda ya kuma bayyana cewa akwai siyasa dangane da matsalar rashin tsaron da ta kwashe lokaci mai tsawo tana addabar jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng