Gwamnan Anambara Ya Fadi Albashin da Ya Kamata a Biya ’Yan Siyasa a Najeriya

Gwamnan Anambara Ya Fadi Albashin da Ya Kamata a Biya ’Yan Siyasa a Najeriya

  • Gwamnan jihar Anambara, Charles Soludo ya fadi kudin da ya kamata gwamnati ta rika biyan yan siyasa albashi a kowane wata
  • Gwamna Charles Soludo ya fadi haka ne yayin da takaddama taƙi karewa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin Najeriya
  • Har ila yau, Charles Soludo ya kuma bayyana irin halin kunci da talakawa ke ciki a kasar inda yace abu kadan zai iya fusata su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambara, Charles Soludo ya yi kira kan a rage albashin da yan siyasa ke diba a Najeriya.

Gwamna Charles Soludo ya fadi haka ne yayin da aka kasa cimma matsaya kan karin albashi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Gwamna Charles Soludo
Gwamnan Anambara ya bukaci a rage albashin 'yan siyasa. Hoto: Charles Soludo
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Soludo ya yi jawabin ne a jiya Laraba yayin wani taro kan murnar ranar dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin yan siyasa a Najeriya

Gwamnan Anambara, Charles Soludo ya ce ya kamata a fara biyan yan siyasa da mafi ƙarancin albashi da ake kokarin samarwa a Najeriya, kamar yadda rabaran Mbaka Ejike ya buƙata.

Ya ce hakan zai taimaka wajen rage kudin da Najeriya ke kashewa musamman a yanzu da ake cikin matsin tattalin arziki.

Yan siyasa sun talauta Najeriya

Gwamna Charles Soludo ya kara da cewa rayuwar almubazzaranci da yan siyasa ke yi na kara ruguza tattalin Najeriya.

Saboda haka Soludo ya yi kira kan a rage musu albashi domin su ɗanɗana halin da talakawa suke ciki ko za su hankalta.

Soludo: Kar a fusata talakawa

Charles Soludo ya bayyana cewa a halin yanzu yunwa da sauran tarin matsaloli sun yiwa talakawan kasar katutu, rahoton the Cable.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya bayyana nasara 1 da Najeriya ta samu saboda dimokuraɗiyya

Saboda haka ya yi kira ga yan siyasa kan cewa su guji yin abin da zai fusata talakawa domin samun cigaban zaman lafiya a kasar.

Jigawa: Za a kai dalibai karatu waje

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya bayyana shirin dawo da kai dalibai yan asalin jihar karatu kasar waje.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar zartarwar jihar ta amince da dawowa da shirin bayan tsaiko da ya samu na shekarun da dama a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng