Sanusi II Vs Aminu: Babbar Kotu Za Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Sarautar Kano
- Babbar kotun tarayya za ta yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron shari'ar sarautar Kano yau Alhamis, 13 ga watan Yuni
- Aminu Babba Ɗanagundi ne ya kai ƙara gaban kotun yana ƙalubalantar matakin gwamnatin Kano na mayar da Muhammadu Sanusi II
- A zaman shari'ar, lauyoyi sun gwabza kan hurumin kotun wanda a ƙarshe aka tsara yanke hukunci yau Alhamis, 13 ga watan Yuni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A yau Alhamis, 13 ga watan Yuni, babbar kotun tarayya mai zama a Kano za ta yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron kara kan rigimar sarautar Kano.
Idan ba ku manta ba gwamnatin Kano karkashin jagoancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta mayar da Muhammadu Sanusi II kan sarauta a matsayin sarki na 16.
Dalilin shigar da kara kan sarautar Kano
Rahoton Leadership ya ce Aminu Babba Danagundi, daya daga cikin dattawan masarautar Kano da aka tube ya maka gwamnatin Kano a gaban kotun yana neman haƙƙinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗanagundi ya roƙi kotun ta dawo masa da haƙƙinsa wanda yake zargin gwamnatin Kano ta take a lokacin da ta tsige shi daga sarautar Sarkin Dawaki Babba.
Lauyoyi sun yi muhawara sosai kan hurumin kotun tarayya a batun da ya shafi dokar da ta tsige Aminu Bayero a matsayin Sarkin Kano na 14.
Lauyoyin sun gwabza a shari'ar sarauta
Barista M. A. Waziri, lauyan wanda ya shigar da kara, Aminu Danagundi da aka tsige daga Sarkin Dawaki Babba, ya ce kotu na da cikakken hurumin sauraren karar.
Ya kuma kara da cewa ba a yi wa wanda yake karewa adalci ba kafin a tsige shi, don haka an tauye masa hakki, kuma tsarin da aka bi na dawo da Sarki Sanusi II ya saɓa doka.
A ɗaya bangaren, lauyan Sanusi II, Barista Muhmud A. Magaji, ya bukaci kotun da ta yi watsi da duk bayanin mai kara na cewa tana da hurumin ci gaba da shari’ar.
Ya kara da cewa babu shakka majalisar dokokin jihar tana da hurumin gyara, soke ko ma samar da wata doka da ta dace da jihar, rahoton Vanguard.
A ƙarshe dai kotun ta ɗage zaman zuwa yau Alhamis domin yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron shari'ar rikicin sarautar da ke faruwa a Kano.
Yan daba sun tada hargitsi a Kano
A wani rahoton kuma Ƴan daba sun tayar da hargitsi a kasuwar da ke Masallacin idi a Kano bayan gwamnatin jihar ta umarci mutane su tashi.
Gwamnatin Kano ta bai wa ƴan kasuwar wa'adin sa'o'i 48 su tashi daga wurin, amma har yanzu ana ci gaba da hada-hada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng