Shugaba Tinubu Ya Fadi Babban Abin da Tattalin Arzikin Najeriya Ke Bukata

Shugaba Tinubu Ya Fadi Babban Abin da Tattalin Arzikin Najeriya Ke Bukata

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya bai gama ginuwa ta yadda zai tsaya da ƙafafunsa ba
  • Tinubu ya bayyana cewa shekaru da dama an ƙyale tattalin arziƙin ƙasar nan ba tare da yi masa sauye-sauyen da yake buƙata ba
  • Ya bayyana cewa matakan da ya ɗauka domin dawo da shi kan turba suna da wahala, amma sun zama wajibi a ɗauke su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce tattalin arziƙin ƙasar nan bai tsaya da ƙafafuwansa yadda ya kamata ba.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa shekaru da dama tattalin arziƙin Najeriya na buƙatar sauye-sauye waɗanda za su dawo da shi kan turba amma ba a yi su ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki matsaya, zai miƙa sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa

Tinubu ya magantu kan tattalin arzikin Najeriya
Shugaba Tinubu ya yi magana kan tattalin arzikin Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin kai tsaye da ya yiwa ƴan Najeriya a ranar Laraba, domin bikin cikar shekara 25 da samun mulkin dimokuraɗiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya jawabin da Tinubu ya yi a shafinsa na X.

Bola Tinubu a kan tattalin arziƙin Najeriya

Tinubu wanda ya amince da ƙalubalen tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fuskanta, ya yi nuni da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin gyara tattalin arzikin ƙasar.

"Na fahimci matsalolin tattalin arziƙi da muke fuskanta a matsayin al'umma."
"Tattalin arziƙinmu yana cikin tsananin buƙatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan ginshiƙin dogaro kan samun kuɗaɗen shiga daga man fetur."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fusata kan kalaman Atiku da PDP ga Tinubu, ta yi martani mai zafi

"Ayyukan gyare-gyaren da muka fara an yi su ne domin samar da ingantaccen ginshiƙi domin samun ci gaba a nan gaba. Ko shakka babu sauye-sauyen sun kawo wahala."
"Amma duk da haka, su ne sauye-sauyen da ake buƙata domin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan ta yadda zai dawo kan turba, ta yadda kowa zai iya samun damar tattalin arziki, albashin da ya dace."
"Yayin da muke ci gaba da sake fasalin tattalin arziƙi, koda yaushe zan saurari jama'a kuma ba zan taɓa juya muku baya ba."

- Bola Tinubu

APC ta caccaki Atiku da PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP, bisa ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasa kan Shugaba Bola Tinubu.

APC ta bayyana cewa kuskure ne ɗora alhakin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki kan Shugaba Tinubu, inda ta ce Atiku bai faɗin gaskiya ga ƴan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng