Bola Tinubu Ya Ɗauki Matsaya, Zai Miƙa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi ga Majaisa

Bola Tinubu Ya Ɗauki Matsaya, Zai Miƙa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi ga Majaisa

  • Bola Ahmed Tinubu ya shirya tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar tarayya domin ta amince da shi
  • Shugaban ƙasar ya sanar da haka ne a jawabinsa na murnar ranar Demokuraɗiyya yau Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024
  • Tun ranar Litinin kwamitin mafi ƙarancin albashi ya miƙa rahotonsa bayan watanni biyar ana tattaunawa kan batun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai girma shugaban ƙasa ya ce zai miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya nan ba da jimawa ba.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya yiwa ƴan ƙasa a ranar Demokuraɗiyya, 12 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Albashi: Daga karshe Tinubu ya fadi abin da gwamnati za ta biya ma'aikata

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa ya ce zai tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Shugaba Bola Tinubu ya san ana wahala

Tinubu ya ce yana sane da wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta kuma ya buƙaci su daure, sannan su jajirce wajen ƙara tabbatar da tsarin demokuraɗiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya wallafa cikakken jawabin Tinubu a manhajar X.

A yau Laraba, 12 ga watan Yuni, Najeriya ta cika shekaru 25 da dawowar damukuraɗiyya ba tare da samun tangarɗa ba.

Kwamitin albashi ya mika rahoto ga Tinubu

Idan ba ku manta ba a ranar Litinin da ta wuce, kwamitin mafi karancin albashi karƙashin jagorancin Alhaji Bukar Goni Aji ya miƙa rahoto bayan kusan watanni biyar.

Wakilan gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun miƙa tayin N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Sai dai ƙungiyar kwadago ta ƙasa ta rage buƙatarta daga N494,000 zuwa N250,000 a zaman kwamitin na ƙarshe.

Kara karanta wannan

"Ba faɗuwa na yi ba" Bola Tinubu ya yi magana kan abin da ya faru a Eagle Square

Bayan karɓan rahoton ana sa ran Mai girma Tinubu zai ɗauki matsaya kana ya miƙa kudirin dokar sabon albashi ga majalisar tarayya domin ta amince da shi.

Tinubu ya ba ƴan Najeriya haƙuri

Da yake jawabi yau, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ɗauko shi ne mafita a kokarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

"Tattalin arzikinmu ya jima yana buƙatar gyara tsawon shekaru, saboda bai zama daidai ba, an dogara kan man fetur ne kaɗai wajen samun kuɗin shiga.
"Mun ɗauko wannan tsare-tsare ne domin gina makoma mai kyau ga ƙasarmu, duk da suna tattare da wahala amma ya zama wajibi mu jure."

- Bola Ahmed Tinubu.

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya ya shaidawa Legit Hausa cewa ba ya goyon bayan N62,000 saboda ba zai ɗauki ɗawainiyar mutum mai iyali ba a halin tsadar da ke ciki.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a yanzu albashin ma'aikata ba ya zuwa ko ina yake ƙarewa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da zane mafi girma a duniya a ranar dimokuraɗiyya

"Ni dai bana goyon bayan adadin da gwamnati ta amince da shi saboda rayuwa ta yi tsada, idan aka yi albashi ba ya yin mako biyu ya ƙare, ina ma'aikata za su sa kansu?"

A cewarsa, tun da an tuge tallafin mai kamata ya yi a yi amfani da kuɗin wajen inganta walwalar ma'aikata da sauran ƴan Najeriya.

Canjin kudi: Emefiele ya shure umarnin Buhari

A wani rahoton kuma tsohon gwamnan CBN ya kara shiga matsala yayin da bayanai ke ƙara fitowa kan tsarin sauya fasalin Naira.

Tsohon daraktan harkokin kuɗi a CBN, Ahmed Umar, ya shaidawa kotun Abuja cewa Emefiele ya buga kalar sababbin kuɗin da ya ga dama ba wanda Muhammadu Buhari ya amince ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel