Gwamnan Adamawa Ya Yiwa Gwamnatinsa Garambawul, an Sauya Wasu Kwamishinoni
- An samu sababbin sauye-sauye a majalisar kwamishinonin jihar Adamawa bayan Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi wani garambawul
- Sauyin da gwamnan ya yi ya shafi wasu ma'aikatu guda huɗu ne waɗanda aka bayyana kwamishinonin da za su ci gaba da jan ragamarsu
- Gwamnan ya ce ya yi hakan ne da nufin ƙara ƙarfin gwiwar kwamishinonin domin inganta ayyukan da suke yiwa mutanen jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a ranar Litinin ya yiwa majalisar kwamishinoninsa garambawul.
Gwamnan ya yi hakan ne da nufin ƙara ƙarfin gwiwar kwamishinonin domin inganta ayyukan da suke yiwa al'ummar jihar.
Da yake sanar da yiwa majalisar kwaskwarima a ranar Litinin a Yola, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mista Humwashi Wonosikou, ya ce sauye-sauyen sun shafi ma'aikatu huɗu ne nan take, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya yi garambawul a Adamawa
Humwashi Wonosikou ya bayyana cewa a yanzu an mayar da tsohuwar kwamishinar yaɗa labarai, Neido Geoffrey Kufulto muƙamin kwamishinan harkokin mata, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Tsohon kwamishinan kasuwanci, James Iliya ya koma muƙamin kwamishinan yaɗa labarai.
Yanzu Mista Hamajumba Gatugel ya zama kwamishinan harkokin kasuwanci yayin da Misis Wunfe Anthony ta zama kwamishiniyar sufuri.
Gwamnan Adamawa a kan kwamishinoninsa
Gwamna Fintiri ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa kwamishinonin za su iya sauke nauyin da aka ɗora musu.
Gwamnan ya yi gargaɗi game da yin zagon ƙasa, ya kuma buƙaci kwamishinonin da su yi aikinsu yadda ya kamata.
Fintiri ya kuma buƙaci kwamishinonin da abin ya shafa da su yi aiki tare domin an miƙa mulki yadda ya kamata ba tare da samun wata tangarɗa ba.
Gwamna Fintiri ya yi naɗi a Adamawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa, a matsayin Amirul Hajj na aikin Hajjin 2024.
Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Yola, babban birnin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng