Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago Sun Bayyana Matsayarsu Kan Biyan N62,000
- Ƙungiyoyin ƙwadago na iya shiga yajin aikin gama gari a ranar Talata, 11 ga watan Yuni, kan sabon mafi ƙarancin albashi
- Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ƙi amincewa da tayin biyan mafi karancin albashi na N62,000 da N100,000 wanda suka bayyana a matsayin albashin yunwa
- A taron ƙarshe na kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi a ranar Juma’a 7 ga watan Yuni, ƴan ƙwadago sun buƙaci a biya ma’aikata mafi ƙarancin albashi na 250,000
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana cewa ba za ta ƙarbi tayin N62,000 ko N100,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ma’aikatan Najeriya ba.
Ƙungiyar ta haƙiƙance kan cewa sai dai gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Mataimakin babban sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), Chris Onyeka, ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'The Morning Brief' a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nawa ƴan ƙwadago ke so a biya ma'aikata?
Ya ce ƙungiyar ƙwadagon ba za ta amince da batun biyan N62,000 ko N100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Najeriya ba.
Ya haƙiƙance kan cewa har yanzu ƙungiyar tana nan a kan bakanta na gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Ya bayyana cewa ba za su amince da tayin da gwamnati ta yi na biyan N62,000 ko kiran da wasu masana ke yi na a biya N100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.
"Ba mu taɓa tunanin saukowa zuwa N100,000 ballantana N62,000 ba. Har yanzu muna nan a kan N250,000, wannan ita ce matsayarmu."
- Chris Onyeka
Wane mataki za su ɗauka na gaba?
Ya kuma bayyana cewa idan gwamnati da majalisar tarayya ba su yi abin da ya dace ba zuwa gobe (Talata, 11 ga watan Yuni), ƙungiyoyin ƙwadagon za su gana domin yanke shawara kan komawa yajin aiki.
A gobe ne dai wa'adin janye yajin aikin domin ba da damar ci gaba da tattauna na mako guda ke cika.
Abin da gwamnoni za su iya biya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jihohi a Najeriya sun bayyana adadin da za su iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Gwamnonin jihohin sun yi duba tare da nazari kan yanayin tattalin arziƙi, inda suka yanke cewa ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba.
Asali: Legit.ng