ICPC: Kotu Ta Daure Jami’in Shige da Ficen Najeriya Shekaru 7 Kan Zambar N100,000
- Wani jami'in hukumar shige da fice ta kasa ya gamu da fushin kotu bayan da hukumar ICPC ta gufanar da shi kan zambar fasfo
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da Quadri Adeyinka ne kan karbar N100,000 da nufin yiwa wani fasfo
- Sai dai gaza yin wannan fasfo ya harzuka mutumin ya kai karar Mista Adeyinka ga ICPC wanda ta tuhume shi da laifuffuka hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotun birnin tarayya, da ke Apo, ta yanke wa wani Quadri Adeyinka, ma’aikacin hukumar shige da fice ta kasa daurin shekara bakwai a gidan yari.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa (ICPC) ta gurfanar da Mista Adeyinka gaban kotun kan zargin zambar fasfo.
Jami'in kula da hulɗar jama'a kuma kakakin ICPC, Demola Bakare, FSI, ya sanar da hukuncin kotun a shafin hukumar na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC ta gurfanar da jami'in shige-da-fice
Demola Bakare ya ce ICPC ta gurfanar da Mista Adeyinka gaban babbar kotun bisa tuhumar laifuffuka hudu da suka shafi zamba, ha'inci, da cin hanci.
Kakakin hukumar ya ce wadannan laifuffukan sun saba wa dokar hana cin hanci da rashawa ta 2000 da kuma dokar laifuffuka.
Lauyan ICPC, Dr. Osuobeni Akponimisingha a yayin zaman kotun, ya gabatar da hujjoji kan yadda Mista Adeyinka ya damfari wani Ovie Ojeffia kan cewa zai samar masa da fasfo.
ICPC ta jawo an daure jami'in shige-da-fice
An ce Mista Adeyinka ya karbi N100,000 daga Mista Ojeffia, domin buga masa fasfo. Sai dai gaza yin hakan ya sa Ojeffia ya mika lamarin ga ICPC.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari'a Onwuegbuzie ya samu Mista Adeyinka da aikata dukkanin tuhume-tuhume hudu da ake yi masa.
Mai shari'a Onwuegbuzie ya yanke wa wanda ake kara hukuncin dauri a gidan yari na shekara bakwai.
Zanga-zanga ta barke a Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi kan sauke kantoman riko na yankin.
Jagoran matasan, wanda ya zanta da Legit Hausa ya aika muhimmiyar bukata ga gwamnan jihar, Bala Mohammed kan dakatar da shugaban karamar hukumar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng