Gwamnan Plateau Ya Cire Dokar Hana Fita da Ya Sanya, Ya Fadi Dalili

Gwamnan Plateau Ya Cire Dokar Hana Fita da Ya Sanya, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnatin jihar Plateau ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang ta sanar da ɗage dokar hana fita da ta sanya a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar
  • Ɗage dokar hana fitan na zuwa ne watanni shida bayan an sanya ta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar inda suka tafka ta'asa
  • Gwamnan ya ce an ɗage dokar ne domin ba mutane dama su koma gonakinsu biyo bayan dawowar zaman lafiya a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya sanar da ɗage dokar hana fita da ya sanya a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.

Hakan na zuwa ne watanni shida bayan wasu ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyukan Pushit da Sabon-Gari inda suka kashe mutum 13.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi abu 1 da ba zai daina yi ba a Najeriya

Gwamnan Plateau ya dage dokar hana fita
Gwamna Caleb Mutfwang ya dage dokar hana fita a karamar hukumar Mangu Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Hakazalika a yayin harin an jikkata wasu mutane da dama yayin da aka ƙona gidaje da masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Mutfwang ya ɗage dokar?

A wata sanarwa da gwamnan ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da majalisar tsaron jihar, biyo bayan dawowar zaman lafiya a yankin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na gwamnan, Gyang Bere, ta ƙara da cewa matakin zai ba da dama ga mazauna yankin su koma noma a gonakinsu.

Gwamnan ya ƙarfafa gwiwar shugabannin al’umma a cikin addinai da ƙabilan yankin da su ci gaba da yin tuni domin ganin an zauna lafiya da juna a tsakanin mutanensu.

A yayin da yake kira ga mazauna ƙaramar hukumar Mangu da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai, su kuma ci gaba da zama ƴan uwan juna, Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin adalci ga kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga a Kaduna, an hallaka miyagu

Dalilin Gwamna Mutfwang na ƙin fara aiki a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya koka kan yadda gwamnatocin baya suka bar wasu ayyuka da ba a kammala ba a sassan jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta ga buƙatar bayar da sababbin kwangiloli ba a cikin shekarar da ta gabata saboda ya fara aiki domin kammala ayyukan da aka bari domin amfanin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng