Ma’aikatan Lantarki Sun Fusata Gwamnan Enugu, Ya Ba da Izinin Rufe Kamfanin Wutan EEDC

Ma’aikatan Lantarki Sun Fusata Gwamnan Enugu, Ya Ba da Izinin Rufe Kamfanin Wutan EEDC

  • Gwamnatin jihar Enugu ta hannun hukumar raya birnin Enugu (ECTDA) ta rufe hedikwata da ofisoshin kamfanin rarraba wutan EEDC
  • Wannan na zuwa ne makonni bayan EEDC ya aika wa gwamnatin jihar sanarwar datse wutar lantarki da ta shiga gidan gwamnati
  • Kamfanin EEDC ya yi ikirarin cewa ya na bin gwamnatin jihar Enugu bashin kudin wutar lantarki na sama da Naira biliyan 1

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Enugu - Da alama dai gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya fusata da takardar da ya karba daga kamfanin rarraba wutar lantarkin Enugu (EEDC).

Kamfanin EEDC ya aika wa gwamnatin jihar sanarwar datse wutar lantarki da ta shiga gidan gwamnatin jihar saboda gaza biyan bashi.

Kara karanta wannan

Kotu ta dawo da basaraken da El-Rufai ya tuge, ta ci tarar gwamnatin Kaduna N10m

Gwamnan Enugu, Peter Mbah
Gwamnatin Enugu ta rufe kamfanin wutar lantarkin jihar. Hoto: @PNMbah
Asali: Twitter

Kamfanin lantarkin EEDC ya tsokano gwamna

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa makonni kaɗan bayan aika wannan sanarwa, hukumar raya birnin Enugu (ECTDA) ta rufe ofishin kamfanin EEDC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce hukumar ECTDA ta rufe kamfanin EEDC ne da sanyin safiyar ranar Talata gabanin ma'aikatan kamfanin su fara zuwa aiki.

Gwamnatin Enugu ta rufe kamfanin EEDC

A cikin wata sanarwa da kakakin kamfanin EEDC, Emeka Ezeh ya fitar, ya ce ma'aikata sun gaza shiga ofishin saboda hukumar ECTDA ta rufe shi.

A cewar sanarwar:

"Masu gadi ne suke sanar da mu cewa karfe 1:53 na safiyar Talata wasu mutane suka garkame ginin kamfanin, suna iƙirarin gwamnan jihar ne ya ba su umarni."

Kakakin kamfanin ya ce ba ya ga hedikwatarsu, hukumar ECTDA ta kuma rufe kananun ofisoshinsu na yankin Abkpa, Awkunanaw da Ogui.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da kwamishina bayan gano wata baɗaƙala, ya ɗauki mataki

Ya ce wannan matakin ya ba su matuƙar mamaki la'akari da cewa babu wata sanarwa da suka samu daga gwamnatin jihar.

Sanarwar datse wutar gidan gwamnati

Mista Eze ya yi zargin cewa rufe kamfanin EEDC ba zai rasa nasaba da sanarwar da suka fitar na cewa za su datse wutar gidan gwamnati ba.

"EEDC na bin gwamnatin jihar Enugu bashin kudi na sama da Naira biliyan 1. Wannan ba wai kiyasci ba ne, domin kafatanin ma'aikatu da gidan gwamnati na amfani da mita ne.

- Kakakin kamfanin EEDC.

Mista Ezeh ya ce abokan huldar kamfanin da suka ki biyan kudin wutar lantarkin sun hada da gwamnatocin jihohin Enugu, Ebonyi, Anambra, Abia da Imo, in ji rahoton The Cable.

Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar Malawi, Dr. Saulos Chilima da wasu mutum tara sun mutu a wani hatsarin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Zargin kisan kai: Kotu ta umarci gwanatin Kano ta biya Ado Doguwa diyyar N25m

Tun a jiya Litinin ne jirgin mataimakin shugaban kasar ya bace, inda aka gagara gano shi tsawon awanni ana nema, sai a yau Talata aka ga tarkacensa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel