Jam'iyyar APC Ta Samu Nasara a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Yobe

Jam'iyyar APC Ta Samu Nasara a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Yobe

  • Jam'iyyar APC ta samu nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 na jihar Yobe
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wacce ta sanar da sakamakon zaɓen ta ce jam'iyyar ta lashe dukkanin kujerun ƙananan hukumomin
  • Shugaban hukumar zaɓen wanda ya sanar da sakamakon bayan an kammala tattara sakamakon zaɓen ya ce sauran jam'iyyu ba su samu ko kujera ɗaya ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Yobe, ta bayyana cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Hukumar zaɓen ta kuma bayyana cewa jam'iyyar APC ta lashe kujerun kansiloli 178 a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka kammala.

Kara karanta wannan

Kebbi: Hukumar zaɓe ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomi 21

APC ta lashe zaben kananan hukumomin Yobe
Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin jihar Yobe Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

APC ta lashe zaɓe a Yobe

Shugaban hukumar zaɓen, Dakta Mamman Mohammed, shi ne ya bayyana hakan bayan an kammala tattara sakamakon zaɓen, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa sauran jam’iyyun siyasa sun shiga zaɓen amma ba su samu nasarar lashe ko kujera ɗaya ba.

Ana sa ran hukumar zaɓen jihar za ta miƙa takardar shaidar cin zaɓe ga waɗanda suka samu nasara yayin da Gwamna Mai Mala Buni zai rantsar da su a nan gaba.

Me Gwamna Buni ya ce kan zaɓen?

Gwamna Mai Mala Buni yayin da yake kaɗa ƙuri'arsa a garinsa ya bayyana cewa har yanzu yana kan shirinsa na ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ba ya yin adawa da shirin gwamnatin tarayya na ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu.

Kara karanta wannan

"Ku kuka jawo": Jigon NNPP ya fadi kuskuren 'yan Najeriya wajen zaben Tinubu

"Bana yin adawa da ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu. Lokacin da na hau mulki a 2019, shiri na shi ne na ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu."
"Sai dai, abin takaici shida daga cikin ƙananan hukumomi 17 ba su iya biyan albashin ma'aikata, hakan ya sanya aka ci gaba da gudanar da asusun haɗaka."

- Mai Mala Buni

Hanyar da APC za ta riƙa raba muƙamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hanyar da jam'iyyar za ta riƙa bi wajen ba da muƙamai.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa jam'iyyar za ta riƙa amfani da rajistar mambobinta ta yanar gizo domin yin naɗe-naɗe na siyasa a kowane mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel