A Ina Gwamnan Edo Ya Ga N70,000 Na Mafi Karancin Albashi? Shehu Ya Taso Gwamnoni a Gaba

A Ina Gwamnan Edo Ya Ga N70,000 Na Mafi Karancin Albashi? Shehu Ya Taso Gwamnoni a Gaba

  • Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan kin amincewa da gwamnoni suka yi ga tayin mafi karancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikata
  • Sani ya yi mamakin inda gwamnatin jihar Edo ta ke samun kudin da za ta biya N70,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da wasu gwamnatoci suka ce ba za su iya biyan N60,000 ba
  • ‘Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan batun biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar Edo

FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya tambayi ‘yan Najeriya kan inda Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ke samun kudin da zai biya ma’aikatan jiharsa mafi karancin albashi na N70,000.

Legit ta ruwaito a baya cewa gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa biyan N60,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwu ba kuma ba zai dore ba daga wurinsu.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Shehu Sani ya yiwa N62,000 da gwamnati tayi ga ma'aikata fashin baki

Sani ya yi wannan tambaya ne bayan da gwamnonin jihohi suka ki amincewa da tayin karin mafi karancin albashi zuwa N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatarwa Kungiyoyin kwadago.

Shehu Sani ya yi mamakin dalilin da zai sa gwamnoni suka ki mafi karancin albashin N62,000
Shehu Sani ya yi mamakin yadda gwamnoni suka ki tayin albashin N62,000 ga ma'aikata | Hoto: @ShehuSani/@GovernorObaseki
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X, @ShehuSani a ranar Asabar, 8 ga watan Yunin wannan shekarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Daga ina jihar Edo ke samun kudinta da za ta tabbatar da daga mafi karancin albashi zuwa N70,000?”

'Yan Najeriya sun mayar da martini ga Shehu Sani

Legit ta tattara wasu daga cikin martanin 'yan Najeriya game da biyan mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar Edo.

@official_osasb7 ya ce:

"Wannan kyauta ce ta yaudara saboda zaben gwamna na jihar Edo yana nan gabatowa cikin wata uku."

@iammegaken ya ce:

"Jihar Edo ita ce ta fara biyan N40,000 shekaru biyu da suka wuce kafin ta kara zuwa N70,000 a wannan shekarar."

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: 'Yan Najeriya sun gano tushen matsalolin kasa, sun ambaci suna

@valencia_cute5 ta ce:

"Kowace jiha a Najeriya za ta iya biyan fiye da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi idan an so, amma son zuciyar ‘yan siyasa da son kai ba zai bar su su yi abin da ya dace ba, maimakon haka za su ta ba da uzurin karya don rufe gaskiyarsu."

@UIlawagbon ya ce:

"Wa’adin mutum zai kare cikin wata uku yana daga mafi karancin albashi zuwa N70,000. Wa yake kokarin yaudara!"

@waltskillslfc ya ce:

"Gwamnan na kokarin haifarwa sabon gwamna matsala ne kawai."

@tjawiee ya ce:

"Ina ganin zai iya zama alheri ga kasa idan aka yi la’akari da hada jihohin da ba sa tabuka komai wuri daya."

Shehu Sani ya kasafta N62,000 na albashi ga shiyyoyin Najeriya

A wani labarin, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan sabon tsarin gwamnatin tarayya na mafi karancin albashin ma'aikata na N62,000 a kasa baki daya.

Kara karanta wannan

NLC: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya kawo mafita kan mafi ƙarancin albashi a jihohi

Legit ta ruwaito cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta kara tayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N62,000 daga N60,000.

Adadin ya tabbata ne yayin da batun ya fito daga bakin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC masu ci (PGF).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.