Ke Duniya: Ahalin Dan Wasan Kwaikwayon Nollywood, Mr. Ibu Na Neman Taimakon Kudin Binne Shi

Ke Duniya: Ahalin Dan Wasan Kwaikwayon Nollywood, Mr. Ibu Na Neman Taimakon Kudin Binne Shi

  • Marigayi John Okafor zai samu damar a binne shi bayan shafe watanni yana ajiye ba tare da an yi bikin bisonsa ba
  • Ahali, dangi da abokansa na neman taimakon kudade domin tabbatar da an ti bikin binne jarumin wasan kwaikwayon
  • Idan baku manta ba, John ya shafe tsawon lokaci yana jinya kafin daga bisani ya kwanta dama a asibitin Legas

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - An bude shafi a manhajar GoFundMe don neman taimakon kudin jana'izar marigayi dan wasan Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mr Ibu.

Dangin marigayin sun sanar da cewa, za a yi masa jana'izar mamacin a ranar 28 ga Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

'Aikin banza ake yi' Naziru Sarkin Waka ya ragargaji 'yan kirifto masu jiran ta fashe

Mr Ibu ya rasu ne bayan ya sha fama da ciwon zuciya a ranar 2 ga Maris, 2024, a Asibitin Evercare da ke Legas, bayan ya shafe watanni yana jinya.

Dangin Mr. Ibu na neman taimakon yadda za a binne shi
Ana neman taimakon binne Mr. Ibu | Hoto: @realmribu
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taimakon da dangin John Okafor ke nema

Bayan sanarwa da shirin bison na kwanaki biyar, kwamitin tsare-tsaren jana’izar da ya hada da danginsa da abokanansa sun roki jama'a da su ba da gudummawa don ganin an gudanar da jana'izar marigayin cikin nasara.

Sanarwar ta ce:

“Kwamitin tsare-tsaren bison marigayi John Okafor (dangi da abokai) suna neman tallafi daga jama'a don taimaka musu wajen gudanar da jana'izar marigayi jarumin Nollywood cikin nasara.”

Yadda aka tsara tafiyar da bikin bison

A cewar sanarwar, za a fara jana'izar ne a ranar Talata, 25 ga Yuni, 2024, da wasa na musamman tsakanin 'yan wasan Nollywood da kungiyar Rangers International, GistReel ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun kashe yan sanda da mutane da asuba

Haka nan, za a gudanar da tattaki da fitilun kendir don tunawa da dan wasan kwaikwayon a ranar Laraba, 26 ga Yuni; yayin da a ranar Alhamis, 27 ga Yuni za a yi addu'ar fatan hutu a gidan marigayin da ke Eziokwe Amurri a Jihar Enugu.

Haka nan dai za a ci gaba da wannan hidima har zuwa ranar 30 ga watan Yuni, inda za a binne shi gaba daya.

Labarin mutuwar Mr. Ibu isa ga jama’a

A tun farko, wani rubutu da aka buga a Najeriya a shafin sada zumunta na Facebook, game da zargin mutuwar wani fitaccen dan Najeriya, ya fara yawo tun watan Oktoban 2023.

An yi zargin cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, John Ikechukwu Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya mutu.

Mista Ibu wanda haifaffen jihar Enugu ne yana fama da kalubalen rashin lafiya da ya janyo masa rasa kafarsa daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.