Sun Yi Shahada? Masallaci Ya Rushe Kan Mutane Suna Tsaka da Sallah a Najeriya
- Wata majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wani masallacin da ke yankin Papa Ajao a jihar Legas ya rushe a ranar Lahadi, 26 ga Mayu, 2024
- Wannan lamari ya faru ne yayin sallar azahar, inda ake fargabar cewa, mutane da dama sun mutu
- Legas ce jihar da aka fi samun rushewar gine-gine a Najeriya, lamarin da ke daukar hankali ainun har ta kai gwamnati ta fara daukar mataki
Papa Ajao, Jihar Legas - A ranar Lahadi, 26 ga Mayu, an shiga fargabar cewa, mutane da dama sun mutu lokacin da wani masallaci ya rushe a yankin Papa Ajao na jihar Legas.
A cewar rahoton da The Nation ta fitar, masallacin ya rushe ne lokacin da ake tsaka da sallar azahar.
Jaridar ta ce mutane da yawa sun mutu kuma an ciro wasu da suka ji raunuka daga cikin burbushin ginin da ya rushe.
Jaridar The Guardian ma ta rahoto cewa, wannan mummunan lamari ya auku ne da rana, kuma tabbas ya kai ga kashe mutane da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, hukumomin jihar Legas basu fitar da wata sanarwa ba game da wannan al'amari mara dadi.
Rushewar gine-gine a Najeriya
A watan Afrilun 2023, tsohon darakta janar na hukumar SON, Farouk Salim, ya bayyana cewa Najeriya ta fuskanci yawaitar rushewar gine-gine a cikin shekarun da suka gabata.
Ya bayyana cewa alkaluma sun nuna cewa akwai sama da rahotannin rushewar gine-gine 221 a Najeriya.
Ya kuma shaida cewa, hakan ya sanya Najeriya ta zama kasa mafi yawan aukuwar rushewar gine-gine a Afirka, kuma Jihar Legas kadai ta samar da 60% cikin 100% na wannan iftila’i.
Dalilin samun rushewar gine-gine a Najeriya
Salim ya danganta rushewar gine-gine da rashin fitar tsarin gini mai kyau da dai wasu sauran dalilan da ke alaka da ingancin aiki.
Ana daukar Legas a matsayin uwa-uba kan rushewar gine-gine, wanda hakan ya sanya aikin magance wannan matsala ya zama na bukatar gaggawa ga gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu.
Gini ya rushe a jihar Legas, ya danne jama'a
A wani labarin, bene mai hawa Bakwai da ake kan aikin ginawa a Anguwar Banana Island a jihar Legas ya rushe kuma ma'aikata da yawa sun makale a ciki.
Daily Trust ta tattaro cewa zuwa yanzun jami'an kai Agajin gaggawa da dama sun mamaye wurin da ginin ya kife domin kaiwa mutanen da suka makale dauki.
Asali: Legit.ng