'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Katsina, Sun Ceto Mutanen da Aka Sace

'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Katsina, Sun Ceto Mutanen da Aka Sace

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga mutum uku yayin wani artabu da suka yi
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar
  • Ya kuma bayyana cewa jami'an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da mutanen da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun kashe wasu mutum uku da ake zargin ƴan bindiga ne.

Ƴan sandan sun kuma kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Sadiq Abubakar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 8 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fille kawunan mutane a wani sabon hari a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun hallaka ƴan bindiga

"A ranar 7 ga watan Yuni, 2024, da misalin ƙarfe 19:23 an samu labari a hedkwatar ƴan sanda ta Sabuwa cewa ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Duya, unguwar Maibakko, ƙaramar hukumar Sabuwa tare da yin garkuwa da wasu mata."
"Bayan samun rahoton, DPO na Sabuwa, CSP Aliyu Mustapha, tare da haɗin gwiwar ƴan banga, sun garzaya zuwa wurin."

- ASP Sadiq Abubakar

Sanarwar ta ƙara da cewa ƴan bindigan sun buɗe wuta kan jami'an tsaron bayan sun hango su, wanda hakan ya sanya nan da nan suka mayar da wuta wanda inda suka yi nasarar daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutanen.

Bayan an kammala artabun, an gano gawarwakin ƴan bindigan mutum uku daga wajen, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka malamin addini da wasu mutum 4 a Plateau

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Abubakar Musa ya yabawa jami'an tsaron bisa bajintar da suka nuna inda ya jaddada jajircewar rundunar wajen tabbatar da kare rayukan al'ummar jihar.

Ƴan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane da satar shanu a kauyen Gidan-Maga da ke karamar hukumar Malumfashi.

Ƴan sandan sun samu wannan nasara ne bayan wani kiran gaggawa da aka masu cewa ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai farmaki kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng