Sheikh Jamilu Zarewa Ya Bayyana Nau’in Cinikin Kirifto da Ya Haramta a Musulunci

Sheikh Jamilu Zarewa Ya Bayyana Nau’in Cinikin Kirifto da Ya Haramta a Musulunci

  • Shahararren malamin addinin Musulunci mai amsa tambayoyi a yanar gizo, Dakta Jamilu Zarewa ya yi fatawa kan kudin kirifto
  • Dakta Jamilu Zarewa ya yi magana ne kan nau'in ciniki da ake yi ta harkar kirifto wanda yace ya sabawa ka'idojin kasuwanci
  • Shehin malamin ya yi fatawar ne biyo bayan yawaitar tambayoyi da masu harkar kirifto suke yi ga malamai a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Shahararren malamin addinin Musulunci, dakta Jamilu Yusuf Zarewa ya yi fatawa a kan harkar kasuwancin kirifto.

Malamin wanda ya saba amsa tambayoyi a yanar gizo ya ce kasuwancin kirifto nau'i nau'i ne daga cikin akwai wanda ya saɓa shari'a.

Kara karanta wannan

'Aikin banza ake yi' Naziru Sarkin Waka ya ragargaji 'yan kirifto masu jiran ta fashe

Jamilu Zarewa
Dakta Jamilu Zarewa ya yi fatawa kan cinikin kirifto. Hoto: Jamilu Zarewa
Asali: Facebook

Dakta Jamilu Zarewa ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haramtaccen cinikin kirifto

Dakta Jamilu Zarewa ya ce akwai nau'in kasuwancin kirifto da mutum zai sanya kudi kamfani suna juyawa.

Ya kara da cewa idan mutum ya zuba kudi za su rika karuwa ko raguwa bayan kamfanin sun juya su ba tare da ya san a ina kamfanin yake ba, hakan ya sabawa shari'a.

Meyasa cinikin kirifto ya haramta?

Malamin ya ce wannan nau'i na ciniki akwai rashin tabbas a cikinsa saboda ba a san asalin kamfanin da yake juya kudin ba.

Kuma ya ce idan aka rike wa mutum kudi bai san a ina zai samo su ba, dadin dadawa kasashe da yawa ba su dauki kirifto a matsayin kudi ba.

Kara karanta wannan

NLC: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya kawo mafita kan mafi ƙarancin albashi a jihohi

Ya kara da cewa ko da takardun kudi da muke aiki da su idan gwamnati ba ta yarda da su ba sun fita daga sunan kudi.

Malam Zarewa ya bayyana cewa dukkan cinikin da babu tabbas to ya sabawa shari'a kuma ya haramta.

A karshe, ya yi kira ga masu neman karin bayani su duba littafinsa mai suna Haramtattun Cinikayya a Musulunci (60) a shafi na 55.

An tambayi Dakta Zarewa kan mining

A wani rahoton, kun ji cewa mutane sun bijirowa Jamilu Yusuf Zarewa tambayoyi game da hukuncin yin mining da sauran harkokin Crypto a musulunci.

Rahotanni sun nu na cewa malamin ya ce ba zai iya amsa tambayar ba domin har yanzu bai gama bincike ba tukuna, yana jiran amsoshin wasu batutuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng