Katsina: Gwamna Ya Ba Ma’aikata Goron Sallah N45,000, Ya Gindaya Sharuda
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba ma’aikatan jihar kyautar N15,000 da bashin N30,000 domin bikin sallah
- Gwamnan ya ce ma’aikatan za su biya N30,000 cikin watanni uku da za a fara cirewa daga watan Yuli mai kamawa
- Wannan matakin gwamnan na zuwa ne yayin ake shirye-shiryen gudanar da bikin babbar salla a fadin duniya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina – Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya gwangwaje ma’aikata da barka da sallah a jihar.
Radda ya ba da kyautar N15,000 ga duka ma’aikatan jihar yayin da kuma ya ba su bashin N30,000 domin gudanar da salla cikin walwala.
Katsina: Radda ya ba ma'aikata goron sallah
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 8 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce ya dauki wannan matakin ne domin ragewa ma’aikatan jihar halin da ake ciki a fadin kasar.
Katsina: Yadda ma'aikata za su biya kudin
“Ganin yadda babbar sallah ke karatowa, na dauki matakin tallafawa ma’aikata wurin ba su bashin N45,000 hade da goron sallah.”
“Domin saukaka musu biyan kudin cikin sauki, za a cire N10,000 kowane wata har N30,000 a watannin Yuli da Agusta da kuma Satumba.”
“Sannan na ba duka ma’aikatan jihar kyautar N15,000 domin gudanar da bukuwan sallah cikin walwala.”
Dikko Umaru Radda
Gwamnan ya ce hakan zai yi matukar tallafawa ma'aikatan jihar gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala.
Katsina: Radda ya magantu kan matsalar tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi magana kan hanyar magance matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Gwamnan ya jaddada buƙatar gwamnati ta mamaye tare da rage wuraren da ba su ƙarƙashin ikonta.
Ya kuma nuna buƙatar magance matsalar iyakokin ƙasar nan tare da kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, inda ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng