Obasanjo, Yar’adua, Jonathan da Buhari Sun Kashe N16tr a Tallafin Fetur Kafin Tinubu

Obasanjo, Yar’adua, Jonathan da Buhari Sun Kashe N16tr a Tallafin Fetur Kafin Tinubu

Abuja – Kusan tun da aka dawo mulkin farar hula ake kokawa da irin makudan kudin da ake batarwa a kan tallafin man fetur.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Shugabannin Najeriya sun yi ta kokarin cire wannan tallafi da ake biya amma ana zargin cewa har yau tsarin ya zama karfen kafa.

A nan, mun waiwayi adadin kudin da gwamnatocin tarayya suka batar da sunan tsarin tallafin tun daga shekarar 2005 zuwa 2022.

Tallafin fetur
Bola Tinubu yana kokawa da kudin tallafin fetur a Najeriya Hoto: @Modrismalagi
Asali: Twitter

Nawa tallafin man fetur ya cinye?

StatiSense ta kawo adadin abin da sauran shugabanni suka kashe kafin Bola Tinubu wanda ya yi ikirarin cire tallafin a ranar farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Matakai 10 da Gwamna Abba ya dauka wajen ayyana dokar ta baci a kan ilmi a Kano

1. Olusegun Obasanjo (N600bn)

Daga shekarar 2005 zuwa lokacin da ya sauka daga mulki a 2007, Olusegun Obasanjo ya kashe N608bn wajen biyan tallafin fetur.

A shekarun 2005 da 2006, Najeriya ta kashe N351bn da N257bn domin hana fetur tashi.

2. Ummaru Musa Yar’adua (N1.37tr)

Marigayi shugaba Ummaru Musa Yar’adua ya kashe N1.37tr a kan tallafin fetur a lokacin da yake raye a kan mulki daga 2007-2009.

Gwamnatinsa ta kashe N272bn, N631bn da N469bn a kasafin da ya yi a shekarar 2009.

3. Goodluck Jonathan (N6.6tr)

Gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan ta kashe N6.68tr a kan tallafin daga 2010 zuwa 2014.

Jonathan ya fara ne da kasafin N667bn har abin ya kai N2.11tr a 2011. A 2012, 2013 da 2014, an kashe N1.36tr, N1.32tr da kuma N2.2tr.

4. Muhammadu Buhari (N7.9tr)

Shi kuwa Mai girma Muhammadu Buhari ya kashe N7.95tr a wannan tsari daga shekarar 2015 zuwa 2022 da aka yi cikakken kasafi da shi.

Kara karanta wannan

Tarihin mafi karancin albashi daga N125 zuwa N250 har ake maganar N60, 000 a yau

A shekarun farko da ya yi a ofis, Buhari ya kashe N654bn, N240bn, N154bn sai N1.19tr sai kuma N508bn a shekarar 2019 da aka yi zabe.

Bayan ya zarce a mulki ya kashewa tallafin fetur N864bn, N1.43tr, har aka kai N2.90tr a 2022.

Bola Tinubu ya zama shugaban kasa

Kuna da labari cewa daga Mayun 2023 zuwa yau, akwai nasarorin da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu cikin shekara 1 a ofis.

An samu cigaba ta fuskar cigaban tattalin arziki da adadin gangunan man da ake haka a Neja Delta sai dai farashin litar fetur ya tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel