Fargabar Barinsu a Baya ya sa Maniyyatan Aikin Hajji Zanga Zanga a Najeriya

Fargabar Barinsu a Baya ya sa Maniyyatan Aikin Hajji Zanga Zanga a Najeriya

  • Maniyyatan aikin hajji daga Ilorin a jihar Kwara sun yi zanga-zanga kan kokarin barinsu da jiragen da ke jigilarsu ke yi bayan sun shafe kwanaki a zube
  • Maniyyata kimanin 270 ne suka rufe babban titin Ilorin/Ogbomoso/Ibadan bayan sun yi kwanaki biyar su na jiran jirgi, kuma bayan zuwan jirgin ma ba a ce mu su komai ba
  • Amirul hajjin jihar Kwara, Yahaya Oloriegbe ya ba maniyyatan hakuri, inda ya shaida wa manema labarai cewa jirgin ne ya samu matsala, amma ana ta kokarin gyara shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Ilorin- Yayin da maniyyatan aikin hajjin bana daga kasar nan ke samun tashi zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali, batun ba haka ya ke ba ga maniyyata daga Ilorin a jihar Kwara. Kimanin maniyyatan 270 ne suka yi zanga-zanga a ranar Juma'a domin nuna bacin rai kan yadda aka bar su zube a filin jirgin.

Kara karanta wannan

Aikin Hajjin 2024: NDLEA ta kama alhazan Najeriya dauke da hodar Iblis a Legas

Hajji
Maniyyatan aikin hajjin daga Ilorin sun yi zanga-zanga Hoto: Kwara State Government
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa maniyyatan sun rufe babban titin Ilorin/Ogbomoso/Ibadan domin ganin mahukunta sun saurari kokensu.

Rahotanni sun ce maniyyatan sun hana shige da fice daga filin jirgin saman ganin yadda ake kokarin mantawa da lamarinsu.

An gano dalilin yajin aikin

Wani maniyyacin aikin hajji a jihar Kwara, Sadudeen Alapo ya bayyana cewa a kwanaki biyar da su ka yi a filin jirgin, a yammacin jiya ne kawai su ka ga an kawo jirgi guda daya. Ya ce duk da an kawo jirgin, babu wanda ya musu zancen su yi haramar tafiya kasa mau tsarkin, kamar yadda solacebase ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta fitar da jawabi

Amirul hajji a jihar Kwara, Yahaya Oloriegbe ya bayyana cewa an kawo jirgin da niyyar kwashe maniyyatan, amma sai ya samu matsala. Yahaya Oloriegbe ya ba maniyyatan hakuri tare da tabbatar musu za a dauki matakin gyara.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

NDLEA ta kama maniyyata da kwayoyi

A baya mun kawo muku labarin cewa hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wasu maniyyatan aikin hajjin bana da horar iblis a Legas.

Hukumar NDLEA ta ce an gano mutane hudun a wani samame da jami'anta suka kai otal din da maniyyatan su ke su na shirin hadiye ledojin hodar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.