El Rufai: PDP Ta Haɗa Baki da Uba Sani Kan Zargin Tsohon Gwamna, Ta Nemo Mafita
- Jami'yyar PDP a jihar Kaduna ta shiga lamarin binciken Nasiru El-Rufai a jihar Kaduna kan zargin badakala
- Jam'iyyar ta bukaci Gwamna Uba Sani da ya gayyaci hukumomin yaki da cin hanci domin bincike tare da hukunta El-Rufai
- Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar jihar ya kammala bincike tare da fitar da rahoto kan badakalar da El-Rufai ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Jami'yyar PDP a jihar Kaduna ta shawarci Gwamna Uba Sani kan lamarin binciken Nasir El-Rufai.
Jam'iyyar ta bukaci Uba Sani da ya gayyaci hukumomin yaki da cin hanci domin bincikar El-Rufai da hukunta shi.
Kaduna: PDP ta magantu kan binciken El-Rufai
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Abraham Catoh ya fitar a shafin Facebook a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta yabawa Uba Sani da kwamitin Majalisar jihar kan wannan mataki na bincikar El-Rufai da mukarrabansa a Kaduna.
Ta ce wannan zargi da ake yiwa El-Rufai ya tabbatar da korafe-korafen da ta dade tana yi kan yadda ake kashe kudin al'umma a wancan lokaci.
PDP ta shawarci Uba Sani kan El-Rufai
"PDP tana kiran Uba Sani da ya gayyato EFCC da ICPC domin bincike tare da hukunta tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai."
"Jam'iyyar tana bibiyar duka abun da ke faruwa kan lamarin jihar tare da daukar matakai a kowace gaɓa."
"Muna godewa kwamitin Majalisar jihar kan irin wannan jajircewa da ya yi domin bankado gaskiya kan almundahana da aka gudanar a tsohuwar gwamnatin El-Rufai."
- Abraham Catoh
Har ila yau, jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan goyon bayan duka matakan binciken almundahana da Uba Sani zai dauka a jihar.
Kaduna: El-Rufai ya yi martani kan bincikensa
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya yi martani kan zargin badakala a gwamnatinsa a jihar Kaduna.
El-Rufai ya ce wannan ba komai ba ne illa bita da kullin siyasa domin bata masa suna bayan gudanar da gwamnatinsa ba tare da matsala ba.
Asali: Legit.ng