'Yan Bindiga Sun Fille Kawunan Mutane a Wani Sabon Hari a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Fille Kawunan Mutane a Wani Sabon Hari a Jihar Neja

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka mutum bakwai bayan sun farmaki ƙauyukan a tsakanin ranakun Alhamis da Juma'a
  • Maharan da suka kai harin ta'addancin sun kuma fille kawunan mutum biyu da suka hallaka a yayin da suke tafka ta'asarsu a ƙauyukan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Aƙalla mutum 7 ne ƴan bindiga suka kashe a wani sabon harin ta'addanci da suka kai a jihar Neja.

Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a wasu ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

'Yan bindiga sun kai hari a Neja
'Yan bindiga sun hallaka mutum 7 a Neja
Asali: Original

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Neja

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun tare fasinjoji a Yobe, sun hallaka mutum 3

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan da ake zargin ƴan ta’adda ne sun fille kawunan biyu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Kabiru Salihu da Abubakar Karaga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin ƙauyukan da aka kai wa harin a tsakanin ranar Alhamis zuwa Juma’a, akwai Lanta, Bassa, Kasimani, Unguwan-Madi da Makuda da dai sauransu, inda aka ƙona gidaje da dabbobi.

Ɗaya daga cikin majiyoyin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda barazanar tsaro ya ce:

"Baki ɗaya, mutane bakwai ne ƴan Boko Haram suka kashe a Bassa."

Ya ce halin taɓarɓarewar rayuwa a sansanin Erena ya ƙara ta’azzara yayin da ake kai hare-hare a kullum.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar Neja ba kan aukuwar lamarin har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ba a same shi a waya ba.

Kara karanta wannan

Kwale kwale ya kife da masu tserewa harin 'yan bindiga a Neja, mutum 4 sun rasu

Ƴan bindiga sun hallaka ɗan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu, Stanley Akpa Nweze da Arinze Joshua Ugochukwu a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a Ebonyi.

Ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka kashe, Mista Nweze shi ne kansila mai wakiltar gundumar Enuagu a majalisar ƙaramar hukumar Onicha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel