A Karshe, Tinubu Ya Fadi Mafi Karancin Albashi da Zai Iya Biya, NLC Ta Bukaci N250,000

A Karshe, Tinubu Ya Fadi Mafi Karancin Albashi da Zai Iya Biya, NLC Ta Bukaci N250,000

  • Gwamnatin Tarayya ta kara mafi karancin albashi da za ta iya biya zuwa N62,000 bayan shafe awanni tana ganawa
  • Gwamnatin ya kara kuɗin ne daga N60,000 da ta yi alkawarin biya tun farko bayan tsunduma yajin aiki da kungiyar NLC ta yi a ƙasar
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta sauko har N250,000 a matsayin mafi karancin albashi daga N494,000 da ta bukata a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan mafi karancin albashi da za ta iya biya.

Bayan doguwar ganawa da aka yi, a karshe Bola Tinubu ya bayyana N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin za ta biya.

Kara karanta wannan

"Kuɗin sun yi yawa" Gwamnoni sun mayar da martani kan sabon mafi ƙarancin albashi

Tinubu ya sake gabatar da mafi karancin albashi ga NLC
Gwamnati Bola Tinubu ta bayyana N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da za ta biya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ.
Asali: Facebook

Tinubu ya kara daga N60,000 ga NLC

Wannan na zuwa ne bayan N60,000 da ta ce za ta biya a baya wanda kungiyar kwadago ya NLC ta ki amincewa da shi, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kungiyar NLC na neman N250,000 bayan ta sauko daga N494,000 da ta bukata tun farko kafin fara yakin aikin a ƙasar.

Wata majiya daga NLC ta tabbatarwa Punch lamarin bayan kungiyar ta sauko har N250,000 yayin tattaunawar da suka yi a Abuja.

Tinubu: NLC ta yi fatali da N62,000

"Bayan bata mana lokaci sun gabatar da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi wanda ma'aikatu masu zaman kansu suka goyi baya."
"NLC ta rage abin da ta ke bukata zuwa N250,000, wannan abin da gwamnatin ta yi abin kunya ne da takaici."

- Cewar majiyar

Gwamanti ta musanta gabatarwa da N105,000

Kara karanta wannan

Minista ya mika mafi karancin albashin N105,000 ga Tinubu? an fayyace gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata jita-jitar fitar da N105,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Gwamnatin ta yi wannan martani ne bayan an yaɗa cewa Ministan kudi, Wale Edun ya gabatar da lissafin karin albashin ga Bola Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar kwadago ta NLC ta tsunduma yajin aiki domin neman karin albashi ga ma'aikata a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.