Tsohon Kwamishina Ya Fadi Abin da Ke Faruwa Tsakanin El Rufai da Uba Sani
- Ana ta musayar kalamai da tofa albarkacin baki a kan zargin da ake yiwa tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai
- Akwai masu tunanin cewa Uba Sani yana neman juyawa uban gidansa baya bayan ya taimaka masa samun mulki
- Dr. Shehu Usman Adamu ya ce sam ba haka abin yake ba, masanin yana da ra’ayin cewa siyasa dama ta gaji hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Mutane daga garuruwa da dabam-dabam suna ta tofa albarkacin bakinsu game da abubuwan da ke faruwa a jihar Kaduna.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta taso tsohon gwamna watau Nasir El-Rufai a gaba duk da irin gudumuwar da ya ba gwamnati mai-ci.
Fada Uba Sani yake yi da El-Rufai?
Dr. Shehu Usman Adamu wanda ya yi kwamishina a gwamnatin Nasir El-Rufai, ya yi magana a kan dambarwar a shafinsa na X (Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tsakiyar makon nan Dr. Shehu Usman Adamu ya nuna cewa duk da abin da ake gani, lamarin ba fada ba ne kamar yadda ake tunani.
Uba Sani v Nasir El-Rufai
"Nasir El-Rufai da Uba Sani ba fada suke yi ba, kuma ba za su taba yin fada ba har abada, manyan abokai ne."
"Abin da yake faruwa rikicin siyasa ne kurum kuma hakan ba matsala ba ce. Haka ake buga siyasa."
"Ku fahimci bambancin da ke tsakanin fada, cin amana da siyasa sai ku huta."
- Usman Modibbo
Wanene yake son ganin bayan El-Rufai?
Wasu ma’abota X irinsu wani Usman Halliru suna ganin abin da yake faruwa da Nasir El-Rufai a yau ya fi karfin gwamna Uba Sani.
Tsohon kwamishinan ilmin na jihar Kaduna ya nuna wannan zance yana kan hanya, shi dai El-Rufai ya musanya zargin barna.
A shafinsa na X da aka fi sani da Twitter, Bashir El-Rufai ya karfafa batun da wasu suke yi na cewa ana neman ganin bayan El-Rufai.
Duk da tulin zargin da ake yiwa gwamnatinsa, Legit ta lura wasu suna zargin da gan-gan ake neman ganin bayan ‘yan siyasar Arewa.
Shehu Usman Adamu masani ne kuma malamin jami’a, kafin ya yi zurfi a boko ya wakilci mazabar Soba a majalisar dokokin Kaduna.
Shehu Sani ya taso Nasir El-Rufai gaba
Shi dai Sanata Shehu Sani ya ce binciken da 'yan majalisar Kaduna suka yi ya wanke shi da ire-irensa kamar yadda labari ya zo a baya.
Tsohon sanatan ya zargi gwamnatin Nasir El-Rufai da tafka barna daga 2015 zuwa 2023.
Asali: Legit.ng