Yan Bindiga Sun Kai Hari a Arewa, Sun Kashe Yan Sanda da Mutane da Asuba

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Arewa, Sun Kashe Yan Sanda da Mutane da Asuba

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari da suka kashe mutane kimanin 50 a kauyuka daban-daban a jihohin Zamfara da Katsina
  • A yayin harin, yan bindigar sun lalata dukiya mai dimbin yawa da anfanin gonar da mutanen yankin suka tara cikin rumbuna
  • Yan sanda sun tabbatar da faruwar hare-haren tare da bayyana irin matakan gaggawa da suka dauka domin shawo kan lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Zamafara, Katsina - Yan bindiga dauke da manyan makamai sun yi dirar mikiya kan mutane a jihohin Zamfara da Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa sun kashe mutane da dama tare da lalata dukiya mai yawa a garuruwan.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta kama masu damfarar mutane domin sama musu izinin aikin hajji

Yan sanda
An kashe mutane kimanin 50 a Zamfara da Katsina. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe yayin harin har da jami'in tsaron jihar da yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da aka kashe a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun kashe mutane 12 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.

Cikin waɗanda aka kashe har da yan sanda bakwai da mutum daya cikin askarawan da gwamnan jihar ya samar domin inganta tsaro.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewa yan bindigar sun kawo harin ne ana ƙoƙarin sallar asuba kuma sun lalata gidaje, motoci da rumbuna.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Yan bindiga sun kashe sama da mutane 30 a kauyukan karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.

Yan bindigar sun kai jerin hare-hare ne cikin kauyuka sama da 10 a karamar hukumar inda suka saka mutane gudu daga garuruwansu.

Kara karanta wannan

Ruftawar mahakar ma'adani: An ceto wasu a galabaice, gwamnati ta dauki mataki

'Yan bindiga: Bayani daga yan sanda

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yan bindigar sun kai su 300.

Muhammad Shehu Dalijan ya ce za su kara tura jami'an tsaro yankunan domin dawo da zaman lafiya, rahoton Channels Television.

An kamo fursunonin da suka gudu

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCOs) ta tabbatar da tserewar fursunoni 109 daga gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja.

Hukumar ta kuma tabbatar da cafko mutum 10 daga cikinsu tare da taimakon sauran hukumomin tsaro da suka bazama nemansu bayan lamarin ya faru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng