Bayan Fasa Gidajen Yari Kusan 20 a Najeriya, an Fadawa Tinubu Dabarar da Zai Dauka

Bayan Fasa Gidajen Yari Kusan 20 a Najeriya, an Fadawa Tinubu Dabarar da Zai Dauka

  • Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karfafa matakan tsaro a gidajen gyaran halin Najeriya
  • Kiran ya biyo bayan kididdigar da majalisar ta fitar kan cewa an kai hare-hare kimanin 20 gidajen gyaran hali cikin shekaru takwas
  • Har ila yau majalisar ta bayyana irin matakan da shugaban kasar ya kamata ya ɗauka domin ganin an magance faruwar matsalar a gaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Majlisar wakilai ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan tsaurara tsaro a gidajen gyaran halin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa majlisar ta yi kiran ne kan yadda aka samu yawaitar kai hare-hare a gidajen tsawon shekaru ba tare da ɗaukan mataki ba.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Bola Tinubu
An bukaci Bola Tinubu ya dauki mataki bayan yawaitar kai hari gidajen gyaran hali. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ne ya mika kudurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasa gidajen gyaran hali a Najeriya

Kabiru Alhassan Rurum ya kawo kudurin ne biyo bayan yawaitar fasa gidajen gyaran hali da 'yan ta'adda suka yi daga 2015 zuwa 2023.

Rurum ya bayyana cewa a cikin shekaru takwas an fasa gidajen gyaran hali 17 a fadin Najeriya.

A cewarsa hakan ya jawo guduwar 'yan fursuna sama da 7,000 a gidajen gyaran halin da aka fasa cikin shekarun.

Dan majalisar ya kara da cewa a shekarun nan, iska mai karfi ta lalata gidan gyaran hali a Neja wanda ya jawo guduwar fursunoni sama da 118.

Matakin da majalisa ta dauka

Bayan gabatar da kudurin, majalisar ta bukaci Bola Tinubu ya kafa kwamitin sauraron koke koke kan lamarin domin kaucewa faruwarsa a gaba.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Ta kuma bukaci a saka sunayen fursunonin da suke gidajen gyara hali a cikin tsarin rajistan 'yan kasa nan da mako hudu masu zuwa.

An mikawa Tinubu rahoton albashi

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan kudi, Wale Edun ya miƙawa shugaban ƙasa Bola Tinubu rahoton sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya ba ministan wa'adin sa'o'i 48 ya tattara bayanai ya miƙa masa saboda cigaba da tattaunawa da yan kwadago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel