Gwamnatin Tinubu a Faifayi: Ko Ya Cika Manyan Alkawuran da Ya Yi a Cikin Shekara 1?
- Manazarta na cigaba da yin nazari kan alkawuran da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka a lokacin yaƙin neman zabe
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawura da dama musamman wadanda suke da alaka da haɓaka tattalin arziki da inganta rayuwa
- A wannan rahoton, Legit ta yi waiwaye domin duba yadda lamura suka kasance bayan shugaban kasar ya shafe shekara daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara daya kan mulki an cigaba da nazari kan kamun ludayinsa.
Bola Tinubu ya yi alkawura da suka shafi farfaɗo da darajar Naira da inganta tattalin arzikin Najeriya.
Sai dai cikin shekara daya da ya shafe a kan karaga, an samu tangarɗa wajen cikan alkawuran kamar yadda rahoton the Cable ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkawuran da Bola Tinubu ya dauka
1. Farfaɗo da darajar Naira
A lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ana canza Naira a kan Dala a tsakanin N465 da N762.
Amma bayan zuwan Bola Tinubu, farashin ya koma tsakanin N1,339 da 1,520 wanda haka ya nuna shugaban kasar bai tabuka komai ba a wannan ɓangaren.
2. Asusun kudin wajen Najeriya
Asusun kudin wajen Najeriya ya ragu da kashi 6.83% a cikin shekara daya da Bola Tinubu ya yi kan karaga.
Kudin asusun ya ragu daga Dala biliyan 35.09 zuwa Dala biliyan 33.69 wanda hakan yake nuna cewa shugaban kasar bai cika alkawarin da yayi na habaka asusun ba.
3. Saukaka sayen kayayyaki
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin samar da yanayi da zai bunkasa harkar saye da sayarwa tsakanin yan kasa.
Sai dai yadda kaya suka rika tashi a kasuwanni ya nuna bai cika alkawarin ba. Farashin kayan abinci ya tashi da kashi 40.53% a mulkin Tinubu.
Atiku ya ragargaji da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya magantu kan shekara guda da Bola Tinubu ya shafe a karaga.
Atiku Abubakar ya bayyana irin hanyoyi marasa ɓullewa da shugaba Bola Tinubu ya bi wajen kawo Najeriya halin da take ciki a yau.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng