Abubuwan da Ya Kamata Duk Mai Niyyan Layya Ya Kiyaye a Kwanaki 10 Kafin Sallah

Abubuwan da Ya Kamata Duk Mai Niyyan Layya Ya Kiyaye a Kwanaki 10 Kafin Sallah

  • Watan Zul Hijja wata ne da al'ummar Musulmi a fadin duniya suke aikata ibadar layya inda suke yanka dabbobi daban-daban
  • Dukkan ibada a addinin musulunci tana da sharuddan da laduba da aka gindaya da duk wanda zai yi ake so ya bi domin samun lada
  • Malam Umar Shehu Zariya ya yi bayani a kan abubuwan da ya kamata Musulmi da ya yi niyyar yin lahiya ya nisanta a farkon wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bayan ganin wata a jiya Alhamis, yau an wayi gari 1 ga watan Zul Hijja kamar yadda mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar.

Daga cikin ayyukan ibada da al'ummar Musulmi suke gabatarwa a watan Zul Hijja akwai layya da ake farawa ranar 10 ga wata.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini, Alkali Abubakar Zariya zai ƙara aure, ya fadi sunan amaryarsa

Umar Shehu Zariya
Malamin addini ya bayyana abubuwan da ake so mai layya ya nisanta. Hoto: Umar Shehu Zariya
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Mika'il Abubakar Yyg ya wallafa a shafin Facebook, Malam Umar Shehu Zariya ya bayyana abubuwan da ake so wanda zai yi layya ya nisanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zan yi layya: Me zan nisanta a musulunci?

1. Ka nisanci yanke farce

Malam Umar Shehu Zariya ya bayyana cewa dukkan wanda ya yi niyyar layya to dole ya nisanci yanke farce da zarar wata ya kama.

Malamin ya kara da cewa haka hukuncin yake idan mutum ya yi niyya a lokacin da babu kudi a hannunsa amma yana tsammanin samunsu a karshen wata.

2. Ka nisanci yin aski sai bayan layya

Har ila yau malamin ya bayyana cewa bai kamata ga duk wanda zai yi lahiya ya yi aski ba, yin aski kuma ya kunshi aske duk wani gashi a jikinsa.

Malam Umar Shehu Zariya ya ce la'alla hikimar sanya dokokin ita ce koyawa Musulmi zaman hakuri da kuma shirin zaman kabari tunda a can babu yanke farce da aski.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

3. Ka da mai layya ya yanke fatar jiki

A wani bangare kuma, Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid ya kara da cewa ana so mutum ya nisanci yanke duk wata fata ko sashen jikinsa da zarar ya yi niyyar layya.

Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Islamqa da yake amsa tambayoyi.

Za a canza tsarin almajiranci a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta sanar da canza salon yadda tsarin almajiranci ke tafiya wajen shigo da tsare-tsaren zamani.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mai ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsangaya da almajiranci, Aminatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ce ta fadi haka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng