Yadda ya dace Musulmi ya fuskanci kwanaki goma (10) na farkon watan Zhul-Hijja, Daga Sheikh Umar Zaria
Haramain Sharifain da Haramain Live sun ruwaito cewa kasar Saudiyya ta sanar da cewa ba'a samu ganin jinjirin watan Zhul-Hijjah ba.
Wannan ya biyo bayan fita neman jinjirin watan da masana suka yi da yammacin Juma'a.
Saboda haka, ranar Lahadi, 11 ga Yuli zai zama 1 ga watan Zhul Hijjah kuma ranar 20 Yuli zai zama ranar Babbar Sallah.
Yayinda watan zai fara ranar Lahadi, Malamai sun yi bayani kan muhimmancin kwanaki 10 na farko a wannan wata.
Babban Malami, Sheikh Umar Shehu Zariya, ya yi rubutu da dalilin da yasa aka fifita wadannan ranaku.
ME YA SA AKA FIFITA YINNAI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH AKAN WASUNSU???
Daga cikin rahamar Allah Ta'ala Ya na fifita ibada a wasu wurare, kwanaki ko lokuta domin Ya baiwa bayinSa daman samun kusanci da shi da dacewa da rahamarSa. Kamar haka ya fifita kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijja da abubuwa Kamar haka:
1. Allah Ta'ala Ya yi rantsuwa da su inda yake cewa: Ina rantsuwa da Alfijir. Da daruruwa goma suratu al-Fajr aya ta 1 da ta 2.
Imam Ibn Kathir, Rahimahullah, ya ce:
Daruruwa goma da aka ambata a ayan su ne yinnai goma na farkon watan Dhul-Hijja.
A duba Tafsiru al-Qur'anil al-'azeem 8/390.
2. Yinnai goma na farkon watan Dhul-Hijja su ne mafi alheri yinnai na duniya.
An karbo daga Jabir, Radhiyallahu Anhu, ya ce:
Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce: Mafi alherin yinnan duniya su ne kwanaki goma, yana nufin na Dhul-Hijja, sai aka ce masa: koda kwatankwacinsu da mutum ya fita jihadi domin Allah?.
Sai ya ce: "koda kwatankwacinsu ga wanda ya fita jihadi domin Allah, sai dai mutumin da akan turbutse fuskansa da kasa (wato ya yi shahada)" Sahihu al-Jaami'u al-Sagir 1133.
3. A cikin su Allah Ta'ala Ya yi umurni da a ambace Shi.
Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma su ambaci Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu". Suratul Hajj 27.
An samo hadisi daga Abdullahi Bn Umar Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce:
"Babu wasu yinnai mafi girma a wurin Allah kuma mafi soyuwa gare Shi da yake so a yi aiki a cikin su kamar wadannan yinnai goma, don haka idan sun zo ku yawaita fadin laa ilaaha illallahu, Allahu Akbar da Alhamdulillahi a cikin su".
Imam Ahmad ya ruwaito a cikin Musnad din shi 2/75.
4. A cikin wadannan kwanaki ne ake samun ranar Arafa. Wanda a cikin shi ne Allah Ta'ala Ya ke yawan 'yanta bayi daga wuta.
An samo hadisi daga uwar Muminai A'isha, Radhiyallahu anha, ta ce: Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce:
"Babu ranar da Allah Ya ke 'yanta bawa daga wuta kamar ranar Arafa, domin Allah Yana kusantowa sannan ya yi ma Mala'iku alfahari (da mutanen da suke filin Arafa) sannan ya ce: me wadannan suke nufi?".
Muslim ne ya ruwaito 1348.
Asali: Legit.ng